2023: Zawarcin da APC, Peter Obi su ke yi wa Wike ya fara kada hantar jagororin PDP

2023: Zawarcin da APC, Peter Obi su ke yi wa Wike ya fara kada hantar jagororin PDP

  • Shugabannin PDP sun fara jin tsoron Nyesom Wike ya tsallaka zuwa wata jam’iyyar kafin 2023
  • Da alama Nyesom Wike ya sa ran Atiku Abubakar zai dauke shi a matsayin abokin takara a PDP
  • Tun da aka zabi Ifeanyi Okowa, aka fara jin labarin Gwamnan ya na ganawa da ‘yan wasu jam’iyyu

Rivers - Jagororin jam’iyyar PDP sun shiga tashin hankali a dalilin wata sabuwar alaka tsakanin gwamnan Ribas, Nyesom Wike da sauran jam’iyyun siyasa.

An yi tunanin Gwamna Nyesom Wike ne zai zama ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar PDP a 2023, daga baya kurum aka ji labari ya canza.

Tun bayan lokacin da Atiku Abubakar ya sanar da Ifeanyi Okowa a matsayin abokin takararsa, abubuwa su ka fara canzawa daga bangaren Nyesom Wike.

Daily Trust a rahoton da ta fitar, ta ce hankalin ‘yan PDP ya fara tashi a kan abubuwan da ke faruwa na zawarcin Gwamnan da APC da LP suke neman yi.

Kara karanta wannan

Kwankwaso da Peter Obi su na tsere da INEC domin yi wa PDP da APC taron dangi mai-karfi

Wike ya fara samun sababbin abokai

Tun bayan zaben tsaida ‘dan takarar shugaban kasa, gidan Gwamnan da ke kan titin Ada George a garin Fatakwal, kullum cike yake da mutane daga ko ina.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da farko, Gwamnan jihar Ebonyi watau David Umahi aka fara samun labarin ya je gidan Wike. Daga baya sai ga ‘dan takaran shugaban kasa, Peter Obi.

Gwamna Wike
Su Gwamna Wike su na yi wa PDP kamfe
Asali: UGC

Peter Obi wanda Wike ya yi wa kaca-kaca bayan barinsa PDP, ya ziyarci jagoran jam’iyyar hamayyar. Ana zargin ya yi masa tayin ya dawo tafiyarsu ne.

Jaridar ta ce Gwamna Umahi wanda ya nemi takarar shugaban kasa a APC da Obi su na neman ganin yadda za su dauke Gwamnan jihar Ribas daga PDP.

Jam'iyyar PDP ta tura mutanenta

Jim kadan sai Bala Mohammed da wasu jagororin PDP suka gana da Gwamnan. Wannan karo an zo ne da niyyar a lallashi Wike kan abubuwan da suka faru.

Kara karanta wannan

Da dumi-duminsa: Peter Obi ya ziyarci Gwamna Nyesom Wike a Port Harcourt

Atiku Abubakar ne ya aiko tawagar Gwamna Bala Mohammed domin su hana shi barin PDP. Tun bayan zaben tsaida gwani, Wike bai fitar da wani jawabi ba.

Babu wata rigima a PDP - Kakaki

Sakataren yada labaran PDP na kasa, Debo Ologunagba ya bayyana cewa babu wani sabani a jam’iyyarsu, sannan ya musanya jita-jitar da ake ta yadawa.

Debo Ologunagba ya fadawa manema labarai cewa kan ‘ya ‘yan jam’iyyar adawar a hade yake. A cewarsa, an kai wa Wike ziyara ne ba don zai sauya-sheka ba.

Atiku zai yi danne kirji

Kafin yanzu kun ji labari, bayan ya ki daukar Nyesom Wike a matsayin abokin takararsa, Atiku Abubakar ya kafa kwamiti na musamman da zai lallashe sa.

Wannan kwamiti zai yi aikin lallashin Gwamna Wike da sauran wadanda suka yi fushi da PDP. Hakan zai taimaka wajen ganin an yi doke APC a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Atiku ya tura manya su yi wa Wike danniyar kirji domin gudun a samu cikas a 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel