Labari mai dadi: Yajin-aikin Kungiyar ASUU ya kusa zama tsohon labari - Gwamnatin Buhari

Labari mai dadi: Yajin-aikin Kungiyar ASUU ya kusa zama tsohon labari - Gwamnatin Buhari

  • Sanata Chris Ngige ya yi alkawarin ba za a dauki lokaci sosai ba, kungiyar ASUU za ta koma aiki
  • Ministan kwadagon na kasa ya shaidawa manema labarai cewa an kusa cin ma matsaya da ASUU
  • Ngige yace akwai batun karin albashi da IPPIS, kuma za su yi zama da malaman a yau Alhamis

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Ministan kwadago da samar da ayyukan yi na kasa, Chris Ngige, ya tabbatar da cewa ba da dadewa ba za a kawo karshen yajin-aikin 'Yan ASUU.

The Cable ta rahoto Ministan yana mai cewa malaman jami’o’in gwamnati da suka yi wata da watanni su na ta faman yajin-aiki, za su koma bakin aiki.

Mai girma Ministan ya bayyana wannan ne a lokacin da yake amsa tambayoyi daga wajen manema labarai bayan an kammala taron FEC a Aso Villa.

Kara karanta wannan

Yajin-aikin ASUU ya zaburar da Dalibi, ya koma neman na-kai maimakon zaman banza

Da aka tambayi Chris Ngige a game da yajin-aikin kungiyar, sai ya nuna an kusa bude makarantu. Ministan ya ce gwamnati za ta koma zama a ranar Alhamis.

Kamar yadda Punch ta kawo rahoto, Ngige ya ce gwamnatin Muhammadu Buhari za ta duba abubuwan da suka jawo aka rufe jami’o’i, domin warware su.

“Ba za a dade ba za a shawo kan lamarin. Za a shawo kan yajin-aikin ba da dadewa ba.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Chris Ngige
Ministan kwadago, Dr. Chris Ngige Hoto: thecable.ng
Asali: UGC
“Matsalolin da ake fama da su sun shafi harkar kudi, albashin ma’aikata, jin dadi da walwala ne.”
“Mun yi zaman sulhu tare da gayyatar ma’aikatar kudi, ofishin kasafin arzikin tarayya, hukumar albashi na kasa da ma’aikatansu a ranar 1 ga watan Maris.”
“Bayan nan sai ya bayyana cewa akwai sauran abubuwa biyu da suka rage – batun tsarin albashinsu kamar yadda aka yi tun a yarjejeniyar shekarar 2009.”

Kara karanta wannan

An sake samun Gwamnan APC da ya yi wa Tinubu alkawarin kuri’un Jiharsa a zaben 2023

“Yarjejeniyar ta ce duk bayan shekaru biyar, za a sake duba albashinsu, wannan magana ta tsaya.”

- Chris Ngige

Inda gizo ke sakar

An rahoto Ngige yana cewa sabaninsu da kungiyar ASUU bayan haka shi ne maganar IPPIS, malamai sun koka kan manhajar na zaftare masu kudi duk wata.

Ministan ya ce don haka aka nemi malaman jami’an su kawo manhajar da suka kirkira domin biyansu albashi. A nan aka tsaya, amma a yau za a sake yin zama.

Dalibi ya kama sana'a

Saura shekaru biyu Abdussalam Mohammed Chindo ya gama Digiri, amma sai aka samu labari yajin-aikin malaman jami’a ya yi sanadiyyarsa na kama sana'a.

Wannan hazikin dalibin ya yi nazarin halin da ake ciki, don haka ya tashi-tsaye yana hada sinadarin ‘Think Big Bleach’ da yake saidawa kowace gora a N350 .

Asali: Legit.ng

Online view pixel