Labari Da Duminsa: Sanatocin APC 3 Sunyi Watsi Da Tsintsiya Sun Rungumi Laima Da Kayan Marmari
- Sanataci guda uku na jam'iyyar APC mai mulki sun yi murabus daga jam'iyyar sun koma jam'iyyun PDP da NNPP
- Sanatocin da suka bar APCn sune Sanata Babba Kaita (Katsina North), Lawal Yahaya Gumau (Bauchi South), da Francis Alimikhena (Edo North)
- Sanata Ahmad Lawan, Shugaban Majalisar Dattawa ne ya sanar da ficewarsu daga APCn a ranar Talata cikin wasiku da ya karanta a majalisar
FCT, Abuja - Sanatoci uku daga jam'iyyar All Progressives Congress, APC, sun yi murabus daga jam'iyyar mai mulki a kasa kamar yadda The Punch ta rahoto.
Yan majalisar sune Sanata Babba Kaita (Katsina North), Lawal Yahaya Gumau (Bauchi South), da Francis Alimikhena (Edo North).
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yayin da Babba Kaita da Alimikhena sun koma jam'iyyar hamayya ta PDP, Gumau, a bangarensa, ya koma jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP.
Sakon sauya shekarsu da murabus na cikin wasu wasiku mabanbanta uku da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya karanto yayin zaman majalisa.
Abin da wasikun suka kunsa
Wasikar Babba Kaita ta ce:
"A matsayina na sanata mai wakiltar Katsina North, na rubuta don sanarwa a hukumance cewa na yi murabus daga jam'iyyar APC, kuma na yi rajita a jam'iyyar PDP.
"Na yi murabus din ne saboda wariya da masu ruwa da tsaki da Gwamnatin Katsina da Jam'iyya a Jihar Katsina ke nuna min, kasancewa ta cikin kanana mutane.
"Tuni an karbe ni da hannu biyu-biyu a jam'iyyar PDP a Jihar Katsina."
A bangarensa, Sanata Alimikhena, ya yi bayanin cewa ya yanke shawarar yin murabus ne saboda "yawan rikice-rikice da ke adabar jam'iyyar ta APC" musamman a yankinsa, "hakan ya haifar da rabuwan kawunan shugabannin jam'iyar da ya janyo rashin da'a da alkibla."
Sauya shekar yan majalisar ya rage adadin yan majalisar APC daga 70 zuwa 67 a majalisar dattawar a cewar sanarwar da hadimin shugaban majalisar, Dr Ezrel Tabiowo ya fitar.
Sanatan APC Ya Saka Wa Daliget Da Kujerun Hajji Bayan Sun Dawo Masa Da Kudinsa Don Ba Su Zabe Shi Ba
A wani rahoton, Sanata Smart Adeyemi wanda ya wakilci Kogi West a Majalisar Tarayya, ya bada kujerun Hajji ga mutum biyar cikin daligets din da ya bawa kudi amma ba su zabe shi ba a zaben fidda gwani na APC.
Adeyemi ya rasa damar komawa majalisar ne a yayin da ya samu kuri'u 43 a zaben fidda gwanin, hakan yasa ya zo na uku.
Sunday Karimi, wanda ya samu tikitin jam'iyyar ya samu kuri'u 288, yayin da Muyiwa Aina wanda ya zo na biyu ya samu kuri'u 73.
Asali: Legit.ng