Ba ku da tsari: Dan kashenin Jonathan ya fice daga PDP, ya caccaki tsarin jam'iyyar na 2023

Ba ku da tsari: Dan kashenin Jonathan ya fice daga PDP, ya caccaki tsarin jam'iyyar na 2023

  • Godsday Orubebe, wanda ya shahara a yunkurinsa na kawo cikas wajen tattara sakamakon zaben shugaban kasa na 2015 a cibiyar taron kasa da kasa ya fice daga PDP
  • Orubebe ya yi murabus daga matsayinsa na jam’iyyar ta adawa, inda ya bayyana cewa jam’iyyar ba ta shirya kwato mulki a zaben 2023 ba
  • A cikin wasikarsa ta barin PDP, Orubebe ya bayyana cewa zabo Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban kasa, ya sabawa yanayin kasa da tsarin mulkin PDP

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Najeriya - Tsohon ministan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Godsday Orubebe, ya yi murabus daga jam'iyyar PDP mai adawa.

Tsohon ministan ya bayyana matakin nasa ne a wata wasika da ya aikewa shugaban jam’iyyar PDP na kasa Iyorchia Ayu.

Orubebe ya fice daga jam'iyyar PDP, ya fadi dalili
Ba ku da tsari: Dan a mutun Jonathan ya fice daga PDP, ya ce ba za ta karbe mulki a 2023 ba | Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

The Cable ta ruwaito cewa Orubebe ya ce murabus din nasa ya fara tun lokacin fitar da wasikar ficewarsa, inda ya kara da cewa shugaban gundumarsa na karamar hukumar Burutu ta jihar Delta yana sane da matakin da ya dauka.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Kwankwaso ya tabbatar da cewar suna kan tattaunawa da Peter Obi don hada gwiwar NNPP da LP

A cewarsa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Saboda haka, ni, a cikin wannan wasikar ina sanar da ku janyewar da na yi gabadaya daga dukkan ayyukana a matakin unguwa, karamar hukuma, jiha da kasa a jam'iyyar PDP.
"Ina matukar alfahari da kuma jin kai na da kasancewa cikin jam'iyyar siyasa da ta yi nasarar sauya al'umma watsattsa zuwa wadda ke jawo mutunta al'umma a idon kasashe.
"Lokacin da muka fadi zaben shugaban kasa a 2015 a cikin yanayi mara dadi, a takaice dai, na zaci cewa jam'iyyar za ta yi amfani da lokacin adawar don sake kulla dabarun sake karbar mulki a cikin zafin nama."

PDP ba ta shirya tabuka komai ba a 2023 – Orubebe

Orubebe ya bayyana cewa halin da jam’iyyar PDP ke ciki a yanzu bai nuna cewa jam’iyyar ta shirya tabuka wani abu ba a zaben shugaban kasa na 2023 ba, inji PM News Nigeria.

Kara karanta wannan

Dalilin da Yasa na Darzo Okowa A Matsayin Abokin Takarata a 2023, Atiku Abubakar

Idan za ku iya tunawa, Orubebe ya shahara ne a lokacin da ya yi yunkuri na kawo tasgaro a wajen tattara sakamakon zaben shugaban kasa na 2015 a cibiyar taron kasa da kasa dake Abuja.

Ya zargi Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) na wancan lokacin, Attahiru Jega, da nuna son kai, inda ya yi maganganu kuma kafafen yada labaran duniya suka dauka.

Poly Bauchi: Babbar ma'aikaciya ta rasa aikinta bisa shiga siyasa da tallata su Tinubu

A wani labarin, kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Abubakar Tatari Ali a Bauchi, ta dakatar da wata babbar ma’aikaciya, Misis Raliya Kashim, bisa zargin hannu dumu-dumi a shiga siyasar da ya sabawa dokar aikin gwamnati.

Kakakin kwalejin, Malam Maimako Baraya ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Bauchi, Punch ta ruwaito.

Baraya ya ce an dakatar da Raliya ne saboda yi wa wasu ‘yan takarar shugaban kasa da na gwamna kamfen ta shafinta na WhatsApp.

Kara karanta wannan

Okowa: Muhimman abubuwa 12 da baku sani ba game da abokin takarar Atiku a PDP

Asali: Legit.ng

Online view pixel