Lawan vs Machina: Daga Karshe, INEC Ta Bayyana Matsayarta Kan Wanene Halastaccen Dan Takara

Lawan vs Machina: Daga Karshe, INEC Ta Bayyana Matsayarta Kan Wanene Halastaccen Dan Takara

  • Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, a karshe ta bayyana matsayanta kan hallarcin takara tsakanin Ahmad Lawan da Bashir Machina a mazabar Yobe ta Arewa
  • INEC ta ce shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ne kadai ta amince da shi a matsayin dan takara, duk da da farko bai yi takara a zaben fidda gwani na sanata ba
  • A cewar hukumar zaben, ta ce ba ta da ikon kin karbar dan takara da jam'iyya ta mika mata don haka doka ta tanada a yanzu

Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta bayyana matsayanta kan rikici da ya barke kan tikitin takarar kujerar mazabar Yobe ta Arewa tsakanin Bashir Machina da Sanata Ahmad Lawan, Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ka ji da matsalolin da ke kanka: Martanin Tinubu ga Atiku kan shaguben abokin takara

Daf da za a rufe karbar sunayen yan takara daga hannun jam'iyyun siyasa, rikici kan kujerar takarar Yobe ta Arewa a APC ya dauki hankula a yayin da Ahmad Lawan, shugaban majalisar dattawa da Bashir Machina wanda ake ganin ya ci zaben na APC ke ta kai ruwa rana.

Lawan da Machina.
Lawan vs Machina: INEC Ta Bayyana Matsayarta Kan Wanene Halastaccen Dan Takara. Photo: Ahmad Lawan, Bashir Machina.
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sillar rikicin Lawan da Machina

Legit.ng ta tattaro cewa Lawan ya shiga takarar shugaban kasa tare da su mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, Rotimi Amaechi da Asiwaju Tinubu wanda shine ya lashe zaben.

Amma, Lawan zai iya samun damar yin takarar sanata a zaben 2023 ne idan Bashir Machina ya janye ya bada tikitinsa ga shugaban majalisar wanda bai yi takarar zaben fidda gwani na sanata ba saboda yana takarar shugaban kasa a APCn.

Kara karanta wannan

Lauyoyi: Maye Gurbin Machina da Ahmad Lawan Ya Fallasa Goyon Bayan Rashin Bin Dokar APC

An yi wa Machina matsayin lamba ya janye wa Lawan wanda ya shafe fiye da shekaru 20 a majalisar amma bai janye ba.

Kafin hakan, Legit.ng ta rahoto cewa APC ta mika sunayen yan takara ga INEC kuma babu sunan Bashir Sheriff Machina, sai dai an maye gurbinsa da Lawan Ahmad wanda bai yi takara a zaben na fidda gwani na sanata a yankin Yobe ta Arewa ba.

Martanin INEC

Da ta ke martani kan lamarin, INEC ta ce bata da ikon kin karbar sunayen yan takara da jam'iyyun siyasa suka kai mata.

Kwamishinan INEC, Mohammed Haruna, wanda ya yi wannan ikirarin ya ce jam'iyyu na da ikon yin zaben fidda gwani yayin da INEC tana da ikon sa ido a kai don tabbatar an bi dokoki.

Ya ce:

"INEC bata da ikon kin karbar sunayen da jam'iyyun siyasa suka kai mata. Jam'iyyun siyasa ke da wuka da nama wurin yin zaben fidda gwani. Aikin INEC shine sa ido kan zaben ta tabbatar an bi dokokin jam'iyyun, dokokin zabe da kundin tsarin mulki.

Kara karanta wannan

Nasarar APC a Zaben Ekiti Babbar Alama Ce Ta Nasarori Masu Zuwa, Sanata Adamu

"Rahoton mu na iya zama hujja a kotu duk lokacin da dan takara ya kai kara a kotu. Don haka ya rage ga dan takarar ya nemi a bashi takardar rahoto na ainihi don ya gabatar wa kotu a matsayin hujja cewa an saba dokokin da na ambata," a cewar kwamishinan na kasa.

Hakazalika Haruna ya bayyana cewa hukumar zaben kawai tana karbar sunayen ne bisa tanade-tanaden dokar zabe na 2022.

Ya ambaci sashi na 29 (1) na dokar zaben don wanke INEC daga wani zargi.

Sashin ya ce jerin sunaye da jam'iyya ta gabatar don zabe "su zama dole sun fito ne daga zaben fidda gwani da jam'iyya ta yi bisa ka'ida."

Asali: Legit.ng

Online view pixel