Lauyoyi: Maye Gurbin Machina da Ahmad Lawan Ya Fallasa Goyon Bayan Rashin Bin Dokar APC

Lauyoyi: Maye Gurbin Machina da Ahmad Lawan Ya Fallasa Goyon Bayan Rashin Bin Dokar APC

  • Lauyoyi sun yi Allah wadai da yadda jam'iyyar APC ta maye gurbin Bashir Machina da Ahmad Lawan a sunayen 'yan takarar sanantoci da ta aike wa INEC
  • Kamar yadda Pelumi, lauya mai rajin kare hakkin 'dan Adam yace, wannan lamarin yayi karantsaye ga sashi na 84 na sabbin dokokin zabe da Buhari ya saka hannu
  • Ya kara da cewa, wannan lamarin ya fallasa goyon bayan rashin bin doka da jam'iyyar ke yi kuma bai yi biyayya da damokaradiyyar da Buhari ke da'awa a kai ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Pelumi Olajengbesi, lauya mai rajin kare hakkin 'dan Adam, ya ce mika sunan Ahmad Lawan a matsayin dan takarar jam'iyyar APC na kujerar Sanatan Yobe na Arewa ya nuna yadda jam'iyyar bata mutunta kundin tsarin damokaradiyya.

TheCable ta ruwaito yadda Lawan, shugaban majalisar dattawan Najeriya ya shiga jerin sunayen 'yan takarar sanatoci da jam'iyyar ta mika wa INEC duk da ba a yi zaben fidda gwani da shi ba.

Kara karanta wannan

Kai Na Kowa Ne, Kuma Kai Ba Na Kowa Bane: Tinubu Ya Yabawa Buhari Kan Zaben Fidda Gwani

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan da Bashir Machina
Lauyoyi: Maye Gurbin Machina da Ahmad Lawan Ya Fallasa Goyon Bayan Rashin Bin Dokar APC. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bashir Machina, wanda yayi nasarar cin zaben fidda gwanin a yankin, ya jaddada cewa ba zai janye saboda shugaban majalisar dattawan ba.

Lawan ya nemi kujerar shugabancin kasa amma Bola Ahmed Tinubu ya lallasa shi inda ya samu kuri'u 1,271 kuma yayi ram da tikitin takarar shugabancin kasa na jam'iyyar.

A yayin jawabi kan wannan cigaba, Olajengbesi, ya ce dole ne APC ta dena take doka da duka wasu ayyuka da zasu zamo illa ga tsarkin damokaradiyya.

Lauyan ya bukaci Machina da ya nemi hakkinsa a kotu.

"A yanzu da Lawan ya fadi zaben fidda gwani na shugabancin kasa, akwai abun mamaki da yayi watsi da tsarin damokaradiyya kuma ake kokarin saka shi zama 'dan takarar kujerar sanatan Yobe ta Arewa bayan a bayyane yake ba a yi zaben fidda gwani da shi ba," takardar tace.

Kara karanta wannan

Lawan ya tsallake rijiya da baya, sunansa ya maye gurbin na Machina a matsayin dan takarar sanata na APC

"APC ta bai wa kanta kunya tare da tozarta kanta ne inda ta bayyana a matsayin jam'iyya mara gudun abun kunya kuma mara mutunta kundin tsarin damokaradiyya wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ke da'awa a kai.
"Idan aka duba tanadin sashi na 84 na dokokin zaben da shugaban kasa yasa hannu a 2022, APC bata isa ta kakaba kowanne 'dan takara ba balle a wannan lamarin da Machina ya nema kuma yayi nasara yayin da Lawan ke ta neman kujerar shugaban kasa inda ya sha mugun kaye.
"Idan za mu lura, makamanta abubuwa irin haka sun faru da 'yan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar APC kamar su Godswill Akpabio, Dave Umahi da Ibikunle Amosun.
"Dole ne APC ta daina irin wadannan rashin adalcin da lamurran dake barazana ga tsarkin damokaradiyya," yace.

A yayin da Legit ta tuntubi wani lauya mai zaman kansa mai suna Abdulaziz Umar kan lamarin, ya tabbatar da cewa duk da shari'a tana daukar lokaci, amma babu shakka Bashir Machina zai yi nasara a kan Lawan a duk kotun da aka je.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Hatsaniya Ta Barke a Hedkwatar APC Na Kasa, Matasa Na Yi Wa Adamu Barazana

"Lamarin nan babu wani abu a boye. Lawan bai yi zaben fidda gwani ba, shi kuma Machina shi daya tilo yayi kuma ya samu nasara. Ya kuma fito yace ba zai janye ba, don ko janyewar ne ba da baki kawai ake yi ba. Kwatsam sai jam'iyya ta mika sunan Lawan a madadinsa? Ai gaskiya ya nemi hakkinsa a kotu don babu shakka zai yi nasara," lauyan yace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel