Ka ji da matsalolin da ke kanka: Martanin Tinubu ga Atiku kan shaguben abokin takara

Ka ji da matsalolin da ke kanka: Martanin Tinubu ga Atiku kan shaguben abokin takara

  • Dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu ya mayar da martani ga takwaransa na PDP, Atiku Abubakar kan shaguben da ya yi masa na zabar abokin takara
  • Atiku dai ya bayyana cewa mukami irin na shugaban kasa baya bukatar wanda ke jan kafa wajen zabar abokin takararsa
  • Da yake martani, Tinubu ya ce abun takaici ne PDP ta dunga furta irin wannan maimakon mayar da hankali wajen magance rikicinta na cikin gida

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) Alhaji Atiku Abubakar, ya yi shagube ga abokan hamayyarsa kan jinkirin da suka yi wajen samar da abokan takara na dindindin a tsawon lokacin da hukumar zabe ta kasa mai zaman kansu (INEC) ta diban masu.

Kara karanta wannan

Dalilin da Yasa Atiku Ya Gujewa Wike, Ya Zabi Okowa Mataimakinsa a Takarar Zaben 2023

A cikin wani jawabi da ya yi, Atiku ya ce ofishin shugaban kasa baya bukatar mutum mai jan kafa wajen zabar abokin takararsa.

Sai dai kuma, sauran yan takarar da ke neman kujerar shugaban kasa a babban zaben 2023 da suka hada da tsohon gwamnan jihar Lagas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na APC, tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso na jihar NNPP, tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi na LP da sauransu sun zabi abokan takara na wucin gadi ne.

Tinubu and Atiku
Ka ji da matsalolin da ke kanka: Martanin Tinubu ga Atiku kan shaguben abokin takara Hoto: @channelstv
Asali: Twitter

A cikin sanarwar da ya sanyawa hannu, Atiku ya yi shagube ka abokan hamayyarsa musamman daga jam’iyyun APC, NNPP da LP kan abun da ya bayyana a matsayin inda-inda wajen daukar hukunci a lokaci mai muhimmanci na daukar abokan takara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce yana da matukar muhimmanci a mulkin damokradiyya yan takarar da ke neman babban mukami irin na shugaban kasa su zabi abokan takararsu, Thisday ta rahoto.

Kara karanta wannan

Dangin gwamna: Muhimman abubuwa 8 da baku sani ba game da abokin takarar Tinubu

“Ofishin shugaban kasa yana bukatar mutum da baya jan kafa wajen daukar hukunci.
"Shi ya sa a kasashe da suka samu kwarewa a dimokradiyya, batun dan takarar shugaban kasa ya zabi mataimaki da kuma yadda ya zabi mataimakin na bayar da dama a gane yadda yan takara suka shirya tunkarar aikin da ke gabansu."

Da yake martani ta hannun kakakinsa, Tunde Rahman, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya ce abin takaici ne ga PDP ta furta irin wannan zancen, Daily Trust ta rahoto.

Rahman ya bayyana cewa kamata yayi ace PDP ta mayar da hankali sosai wajen magance matsalolinta na cikin gida.

Ya ce:

“Ya kamata PDP ta mayar da hankali wajen magance matsalolinta na cikin gida, sun gaza cika dukkanin alkawaransu na cikin gida.

“Ya kamata su daina kamfen mai cike fa Farfaganda kan tikitin Musulmi da Musulmi, da sauransu.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel