Zaben Ekiti: Nasarar Oyebanji ya nuna APC ta karbu sosai a wajen yan Najeriya – Buhari

Zaben Ekiti: Nasarar Oyebanji ya nuna APC ta karbu sosai a wajen yan Najeriya – Buhari

  • Shugaba Muhamadu Buhari, ya yi wa dan takarar gwamnan Jihar Ekiti na Jam'iyyar APC murnar lashe zaben gwamna da aka yi
  • Buhari ya bayyana cewa wannan nasarar manuniya ce cewa APC ta karbu sosai a wajen yan Najeriya
  • Ya kuma jadadda cewa hakan na nuna jam'iyyar mai mulki za ta yi nasara a babban zaben 2023 mai zuwa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ekiti - Shugaban kasa Muhamadu Buhari, ya taya dan takarar gwamnan jihar Ekiti a karkashin inuwar Jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Biodun Oyebanji, murnar lashe zaben da ya yi.

Shugaban kasar ya kuma taya shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu da kwamitin aiki na jam’iyyar murna kan wannan nasara wanda ita ce ta farko a karkashin sabuwar shugabancin jam’iyyar.

Muhammadu Buhari, shugaban APC, Abdullahi Adamu da zababben gwamnan Ekiti, Oyebanji
Zaben Ekiti: Nasarar Oyebanji ya nuna APC ta karbu sosai a wajen yan Najeriya – Buhari Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

Ya ce:

“Wannan mafari mai kyau ne gareka da tawagarka. Jam’iyyar APC na kara kafi da Karin hadin kai. Nasarar jam’iyyarmu a Ekiti alama ce da ke nuna karfin gwiwar yan Najeriya a iyawar jam’iyyarmu mai albarka wajen kawo shugabanci mai inganci gare su.”

Kara karanta wannan

Dangin gwamna: Muhimman abubuwa 8 da baku sani ba game da abokin takarar Tinubu

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Buhari a wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, 19 ga watan Yuni, ya bukaci ‘ya’yan jam’iyyar mai mulki na gida da waje da su dauki wannan nasarar da aka samu a matsayin manuniya nasarar APC a babban zabe mai zuwa.

Shugaba Buhari ya yaba wa Oyebanji kan nasarar da ya samu a zaben yana mai cewa ya cancanci ya zama gwamna saboda irin gudunmawar da ya bayar wurin kawo ci gaba a Jihar Ekiti da kuma Jam'iyyar APC a jihar tun kafin ya zama dan takara.

Buhari ya kuma bukace shi da ya kasance mai alkhairi domin amfanin al’ummar jihar.

Ya jadadda cewar APC na kara karfi tare da karin hadin kai, yana mai cewa nasarar alama ce da nuna yan Najeriya na da karfin gwiwa kan jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Abokin takarar Tinubu: Kungiyar APC ta tsayar da gwamnan Neja, Sani Bello

Manyan dalilai 3 da suka sanya APC ta lashe zaben gwamnan Ekiti

A baya mun kawo cewa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana Biodun Oyebanji na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Ekiti na 2022.

Oyebanji ya samu jimlar kuri’u 187,057 wajen kayar da manyan abokan takararsa – Segun Oni na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) da Bisi Kolawole na jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP).

Jam’iyyar SDP ce ta zo ta biyu da jimilar kuri’u 82,211 yayin da PDP ta zo ta uku da kuri’u 67,457.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng