2023: Wike Ya Lashe Zaben Kwamitin Shawari Na Zaben Mataimakin Atiku a PDP

2023: Wike Ya Lashe Zaben Kwamitin Shawari Na Zaben Mataimakin Atiku a PDP

  • Kwamitin shawara da jam'iyyar PDP ta kafa domin taimakawa wurin zaben abokin tafiyar Atiku Abubakar, ya yi karamin zabe
  • Gwamna Wike na jihar Ribas, daya daga cikin 'yan takara ukun ya yi nasarar lashe zaben bayan ya samu kuri'u mafi rinjaye
  • Gwamnan jihar Ribas din ya samu kuri'u 16 daga cikin 19 inda ya lallasa sauran 'yan takara biyun da ake duban ko za a dauko su

FCT, Abuja - Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya yi nasarar lashe zaben da majalisar shawara da PDP ta kafa domin taimakawa wurin zabo abokin tafiyar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Daily Trust ta rahoto cewa, majalisar ta yi karamin zaben ne ga mutum ukun da aka gabatar da sunayensu domin saukake wahalar da ake ta sha wurin zakulo wanda ya cancanta a yi tafiyar da shi.

Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas
2023: Wike Ya Lashe Zaben Kwamitin Shawari Na Zaben Mataimakin Atiku a PDP. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

An tattaro cewa, Gwamna Wike ya yi nasarar lashe kwarya-kwaryan zaben da aka yi a hedkwatar jam'iyyar PDP ta Abuja.

Legit.ng ta tattaro cewa, an kafa kwamitin shawarar ne domin sake duba rahoton da kwamitin Janar Aliyu Gusau ya fitar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kwamitin Gusau ya zabo gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike da Gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel domin a zaba daga cikinsu.

An tattaro cewa, kwamitin, wanda shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu, ya kafa a ranar Talata, 14 ga watan Yuni, ya fara aiki a take.

An gano cewa, a zaben da aka yi a sirrance, Wike ya samu kuri'a 16 daga cikin jimillar 19.

Daily Independent ta ruwaito cewa, duk da mafi rinjayen 'yan kwamitin sun zabi Gwamna Wike, Atiku ne zai yanke hukuncin ko zai yi tafiyar da shi ko a'a.

Mambobin kwamitin da ya samu shugabancin mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa daga arewa, Ambasada Damagum, su ne: Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue, Aminu Tambuwal na jihar Sokoto, Bala Mohammed na jihar Bauchi, tsohon gwamnan Niger Babangida Aliyu, Sule Lamido na jihar Jigawa, Liyel Imoke daga Cross Rivers da sauransu.

Abokin tafiyar Atiku: PDP ta rage, tana duba hada Atiku da daya cikin wasu jiga-jigai 3

A wani labari na daban, a yayin da babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta kammala tantance abokin dan takararta na shugaban kasa, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, a yau, jam’iyyar na iya tunanin zabar dan takarar mataimakin shugaban kasa a zaben 2023.

Bayan da Atiku ya samu tikitin tsayawa takara, ana sa ran zai fitar da dan takarar da zai samu karbuwa ga dukkan bangarorin kasar nan, wanda zai iya tattaro kuri'u daga yankin Arewa da Kudu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel