Zaben Ekiti: Bidiyon Samamen Da EFCC Ta Kai Ta Kama Wasu Da Ake Zargin Suna Siyan Kuri'a

Zaben Ekiti: Bidiyon Samamen Da EFCC Ta Kai Ta Kama Wasu Da Ake Zargin Suna Siyan Kuri'a

  • Jami'in hukumar yaki da rashawa ta EFCC sun cafke wasu mutane da ke zargi da siyan kuri'u a yayin zaben gwamna na Ekiti
  • An kama mutanen ne dauke da wasu makuden kudade da ake zargin suna amfani da shi wurin siyan kuri'un
  • Jami'an na EFCC sun tisa keyar mutanen zuwa ofishin rundunar yan sanda inda aka yi holensu kuma za a zurfafa bincike

Jihar Ekiti - Jami'an Hukumar yaki da rashawa da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annarti EFCC, ta kama wasu mutane da ake zargi da hannu wurin siyan kuri'u a zaben gwamna na Ekiti.

An kama mutanen da ake zargin ne a wani gida dauke da kudade masu yawa da ake zargin na siyan kuri'u ne zaben kamar yadda ya ke a bidiyon.

Kara karanta wannan

Muhimman Abubuwa 10 da Ya Dace a Sani Game da Zaben Gwamnan Ekiti

EFCC na cikin jami'an tsaro da suka tura jihar domin su sa ido kan yadda zaben ke gudana.

Wasu da EFCC ta kama kan zargin siyan kuri'a a Ekiti.
Zaben Ekiti: Bidiyon Samamen Da EFCC Ta Kai Ta Kama Wasu Da Ake Zargin Suna Siyan Kuri'a. Hoto: @ChannelsTV.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da suke holen wasu mutane da ake zargin a ofishin yan sanda na Oke Ori Omi, hukumar ta ce an kama wadanda ake zargin ne tare da kudi da ake zargin ana amfani da shi wurin siyan kuri'u, abin da EFCCn ta ce ana yi a boye.

Daga bisani jami'an na EFCC sun kuma kai samame wani gida inda aka kama wasu mutane da wani littafi da ke dauke da sunaye da bayanan masu zabe a wani yanki.

EFCC Ta Kama Tsohon Gwamna Da Matarsa Kan Zargin Rashawa

A wani labarin, mun kawo muku cewa Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta kama tsohon gwamnan jihar Nasarawa kuma sanata mai ci a yanzu, Tanko Al-Makura da matarsa kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari: Sai mun rukurkusa duk masu cin gajiyar rashin tsaron kasar nan

Majiyoyi daga hukumar yaki da rashawar sun shaidawa Premium Times cewa a halin yanzu jami'an EFCC na yi wa tsohon gwamnan da matarsa tambayoyi a hedkwatar ta da ke Abuja.

Duk da cewa ba a samu cikaken bayani kan dalilin kama tsohon gwamnan da matarsa ba, majiyoyi sun ce kamun na da nasaba da zargin cin amana da bannatar da kudade da gwamnan yayi yayin mulkinsa na shekaru takwas a matsayin gwamnan Nasarawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel