Da Dumi-Dumi: EFCC Ta Kama Tsohon Gwamna Da Matarsa Kan Zargin Rashawa

Da Dumi-Dumi: EFCC Ta Kama Tsohon Gwamna Da Matarsa Kan Zargin Rashawa

  • Hukumar EFCC ta kama tsohon gwamnan jihar Nasarawa Tanko Al-Makura da matarsa
  • Majiyoyi daga EFCC sun bayyana cewa an kama shi ne bisa zargin bannatar da kudi da cin amanar jihar yayin da ya ke gwamna
  • Danjuma Joseph, ya ce bai da masaniya a kan cewa EFCC ta kama mai gidansa a yayin da aka tuntube shi

Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta kama tsohon gwamnan jihar Nasarawa kuma sanata mai ci a yanzu, Tanko Al-Makura da matarsa kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Majiyoyi daga hukumar yaki da rashawar sun shaidawa Premium Times cewa a halin yanzu jami'an EFCC na yi wa tsohon gwamnan da matarsa tambayoyi a hedkwatar ta da ke Abuja.

Da Dumi-Dumi: EFCC ta kama tsohon Gwamna Da Matarsa Kan Zargin Rashawa
Da Dumi-Dumi: EFCC ta kama tsohon Gwamna Da Matarsa Kan Zargin Rashawa
Asali: Original

Duk da cewa ba a samu cikaken bayani kan dalilin kama tsohon gwamnan da matarsa ba, majiyoyi sun ce kamun na da nasaba da zargin cin amana da bannatar da kudade da gwamnan yayi yayin mulkinsa na shekaru takwas a matsayin gwamnan Nasarawa.

Kara karanta wannan

Na gwammace in mutu da na bai wa Fulani filin kiwo, in ji wani Gwamna

Al-Makura ya rike mukamin gwamnan Nasarawa daga 2011 zuwa 2019 kafin aka zabe shi a matsayin sanata mai wakiltar mazabar Nasarawa ta Kudu a jihar.

Da aka tuntube shi game da batun, kakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren ya ce kawo yanzu ba a masa bayani a kan lamarin ba.

Mene tsohon kakakin Al-Makura ya ce game da lamarin?

Tsohon mai magana da yawun gwamnan, Danjuma Joseph, ya ce bai da masaniya a kan lamarin a yayin da aka tuntube shi.

Joseph ya ce:

"Mai girma ya bar Lafia (babban birnin jihar Nasarawa) a safiyar yau don zuwa Abuja. Bani da labarin an kama shi."

Hukumar ta EFCC bata taba bincikan tsohon gwamnan ba a baya.

Hasali ma, hukumar ta EFCC ta taba taimakawa gwamnan da iyalansa a lokacin da wani dan damfara ya ya yi kokarin damfarar gwamnan a 2018.

2023: Ku Tashi Ku 'Ƙwace' Mulki Daga Hannun Dattijai, Gwamna Ya Zaburar Da Matasan Nigeria

Kara karanta wannan

Ku Tona Min Asiri Idan Har Na Saci Kuɗin Talakawa, Gwamnan Nigeria Ya Faɗa Wa Masu Zarginsa

A wani labari daban, Yahaya Bello, Gwamnan Jihar Kogi ya ce matasan Nigeria ba su nuna wa dattijai cewa 'lallai da gaske suke son karɓe shugabancin kasa ba', rahoton The Cable.

Bello, wanda tuni ya bayyana niyyarsa na yin takarar shugabancin kasa, a ranar Talata ya yi kira ga matasa su yi aiki don ganin sun 'ƙarbe' mulki daga hannun dattawa gabanin zaben 2023.

Gwamnan ya yi wannan kiran ne a ranar Talata a Ijebu-Ode, jihar Ogun, a wurin wani taro da aka yi wa laƙabin: "Matasa ke da iko a hannun su'.

Asali: Legit.ng

Online view pixel