Zaben Ekiti: An Harba Bindiga Daga Fadar Sarkin Garinsu Dan Takarar Gwamna Na Jam'iyyar SDP

Zaben Ekiti: An Harba Bindiga Daga Fadar Sarkin Garinsu Dan Takarar Gwamna Na Jam'iyyar SDP

  • A yayin da ke gudanar da zaben gwamnan Jihar Ekiti a yau Asabar, an ji karar harbin bindiga daga fadar sarkin garin su Segun Oni
  • Ko da yake karar harbin bindiga a lokacin zabe alama ce da ke nuna akwai tashin hankali ko matsala, a wannan karon sarkin garin ne ya farka
  • Segun Oni shine dan takarar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) a zaben gwamnan kuma zai kada kuri'arsa ne a karamar hukumar Ifaka Ekiti

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Ekiti - An ji karar harbin bindiga daga fadar sarkin Ifaki, garin su Cif Segun Oni, dan takarar gwamna na jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) a zaben Ekiti da ke gudana, Daily Trust ta rahoto.

A yayin zabe, jin karar harbin bindiga alama ce ta tashin hankali amma a wannan karon, alama ce da ke nuna sarki ya farka daga barci.

Kara karanta wannan

Gwamnan Ekiti: Ba za mu karbi kudi ba, masu zabe sun dage, sun zargi APC da hauro da mutane don su yi zabe

Mutane na kada kuri'a.
Zaben Ekiti: An Harba Bindiga Daga Fadar Sarkin Garinsu Dan Takarar SDP. Hoto: @TheNationNews.
Asali: Depositphotos

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana gudanar da zaben a kananan hukumomi 16 da ke Jihar ta Ekiti. Duk da cewa akwai yan takara guda 16 a zaben, hankula ya fi karkata ne ga jam'iyyu uku - jam'iyyar APC mai mulki, jam'iyyar PDP da SDP.

Yayin da APC ta tsayar da tsohon sakataren gwamnatin jihar Ekiti, Biodun Oyebanji a matsayin dan takararta, PDP ta tsayar da tsohon ciyaman dinta na jihar, Bisi Kolawole a matsayin mai rike mata tuta, yayin da SDP ta tsayar da tsohon gwamnan jihar, Segun Oni.

Oni zai kada kuri'arsa a gunduma ta 4, mazaba ta 6 a karamar hukumar Ifaka Ekiti.

Ekiti 2022: 'Idan Ba Kuri'a, Ba Kudi', Bidiyon Tinubu Yana Yi Wa Masu Zabe Ba'a a Wurin Kamfen

A bangare gudan, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a zaben 2023, Asiwaju Bola Tinubu, ya bukaci al'ummar Jihar Ekiti su fito su yi zabe idan ba hakan ba ba za a biya su ba.

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnan Ekiti: Mazauna Jihar Sun Bayyana Wadanda Za Su Zaba

Tinubu, wanda ya ziyarci a Jihar Ekiti a ranar Talata ya furta hakan ne wurin yakin neman zabe na dan takarar gwamna na jam'iyyar, Biodun Oyebanji gabanin zaben da ake shirin yi ranar Asabar 18 ga watan Yunin 2022.

Ya kuma kambama kansa cewa bai taba fadi zabe ba a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel