Zaben Gwamnan Ekiti: Mazauna Jihar Sun Bayyana Wadanda Za Su Zaba

Zaben Gwamnan Ekiti: Mazauna Jihar Sun Bayyana Wadanda Za Su Zaba

  • Wasu mazauna garin Ekiti sun bayyana yan takarar da za su zaba awanni kafin zaben gwamna a jihar na 2022
  • A cewar wasu da dama cikin masu zaune a jihar, yan takarar jam'iyyun APC, PDP da SDP ne suke ganin za su iya lashe zaben
  • Sai dai, jam'iyyun siyasa guda 16 ne za su fafata a zaben da za a yi a ranar 18 ga watan Yuni a jihar

Ekiti - Gabanin zaben gwamnan Jihar Ekiti, mazauna jihar wadanda suka yi magana da Legit.ng sun bayyana yan takarar da suka fi so a cikin wadanda ke neman kujerar gwamnan jihar.

Akwai yan takarar gwamna guda 16 da suka shiga takarar na neman gaje kujerar Gwamna Kayode Fayemi.

Kara karanta wannan

2023: Jerin abubuwa 5 da su ka jawo Atiku ya ki daukar Wike, ya zabi Okowa a PDP

Gwamna Kayode Fayemi na Jihar Ekiti.
Ekiti 2020: Mazauna Jihar Sun Bayyana Wadanda Za Su Zaba. @thecableng.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu cikin yan takarar su ne: Oluwole Oluyede na African Democratic Congress (ADC); Kemi Elebute Halle na Action Democratic Party (ADP); Biodun Oyebanji na All Progressives Congress (APC); Olabisi Kolawole na Peoples Democratic Party (PDP); tsohon gwamna Segun Oni, na Social Democratic Party (SDP) da Ranti Ajayi daga Young Progressives Party (YPP).

Da ya ke magana da Legit.ng, Dare Ajewole ya ce shi kam zai zabi Olabisi Kolawole na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) saboda ya yarda da tsohon gwamna Ayodele Fayose. A cewarsa, idan Fayose ya yarda da dan takarar, shi ma ya yarda da shi.

Wani mazaunin jihar wanda ya ki bayyana sunansa ya ce zai zabi Injiniya Segun Oni na jam'iyyar Social Democratic Party (SDP). A cewarsa, iyayensa sun ji dadi a lokacin da Oni ke gwamna a jihar.

Kara karanta wannan

2023: Jigon PDP Zai Yi 'Murabus' Saboda Atiku Ya Zabi Okowa a Matsayin Mataimakinsa, Zai Koma Yi Wa Tinubu Kamfen

A bangarenta, Madam Adeyeye Morenikeji ta ce za ta zabi dan takarar jam'iyyar APC mai mulki a jihar. Ta ce gwamnati mai zuwa za ta cigaba da ayyukan da gwamnati mai ci yanzu ke yi. Ta koka kan cewa rashin cigaba a gwamnati yana janyo wa jihar matsaloli.

Ekiti 2022: 'Idan Ba Kuri'a, Ba Kudi', Bidiyon Tinubu Yana Yi Wa Masu Zabe Ba'a a Wurin Kamfen

Tunda farko, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a zaben 2023, Asiwaju Bola Tinubu, ya bukaci al'ummar Jihar Ekiti su fito su yi zabe idan ba hakan ba ba za a biya su ba.

Tinubu, wanda ya ziyarci a Jihar Ekiti a ranar Talata ya furta hakan ne wurin yakin neman zabe na dan takarar gwamna na jam'iyyar, Biodun Oyebanji gabanin zaben da ake shirin yi ranar Asabar 18 ga watan Yunin 2022.

Kara karanta wannan

2023: Ba A Ga Wike Ba A Wurin Taron Gabatar Da Okowa A Matsayin Mataimakin Atiku

Ya kuma kambama kansa cewa bai taba fadi zabe ba a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel