Janar Abdulsalami Abubakar ya bayyana matsala 1 da za a iya samu a zaben 2023

Janar Abdulsalami Abubakar ya bayyana matsala 1 da za a iya samu a zaben 2023

  • Hankalin kwamitin National Peace Committee (NPC) ya tashi da zaben Gwamnan Ekiti ya gabato
  • Shugaban NPC, Janar Abdulsalami Abubakar ya na tsoron a saye kuri’un Bayin Allah a zaben 2023
  • Abdulsalami Abubakar sun lura ne da yadda ‘yan siyasa suka kashe kudi a zaben fitar da gwani

Abuja - Kwamitin zaman lafiya na National Peace Committee (NPC) da Abdulsalami Abubakar yake jagoranta, yana da shakku game da zaben 2023.

Daily Trust ta ce Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya) a matsayin shugaban kwamitin na kasa, ya na tsoron ayi amfani da dukiya wajen cin zabe.

Dattijon ya ce wannan mummunar dabi’a da ke neman zama ruwan dare za ta iya lalata ingancin zaben shekara mai zuwa da ake son ganin an yi adaci.

Zaben jihar Ekiti

Abdulsalami Abubakar ya bayyana wannan ne a wani jawabi na musamman da ya fitar da sa hannunsa game da batun zaben gwamnan jihar Ekiti.

Kara karanta wannan

Biyu Babu: INEC Tayi Watsi da Sunan Akpabio a Matsayin 'Dan Takarar Sanatan APC

Idan ba a manta ba, a ranar 18 ga watan Yunin nan na 2022 za a zabi sabon gwamna a jihar Ekiti.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamitin na NPC mai burin ganin an yi zabe lafiya kalau ya hango zaben 2023 zai iya zuwa da tangarda saboda yadda aka rika yin amfani da dukiya.

Abdulsalami Abubakar
Janar Abdulsalami Abubakar a Aso Villa Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

An yi facaka a zaben gwani

Janar Abdulsalami ya nuna masu neman takara sun kashe kudin hauka saboda samun tikiti a zaben fitar da gwanin da aka shirya a kwanakin baya.

“Mu na da masaniya cewa watakila zaben 2023 ba zai zama wanda ya fi kowane kyau ba, kamar yadda aka ga irin amfani da kudi da aka yi a harkar.”
“An samu hatsaniya wajen gudanar da zaben fitar da gwani, kuma an daga martabar masu zaben ‘dan takara fiye da na sauran al’ummar kasar nan.”

Kara karanta wannan

2023: Watakila Bola Tinubu ya dauki Musulmi a ‘Dan takarar Mataimakin Shugaban kasa

- Abdulsalami Abubakar

Sun ta ce kwamitin ya samu damar kira ga mutanen jihar Ekiti da su kauracewa rigingimin zabe, su nemi a zauna lafiya ba tare da an samu wata matsala ba.

Da zaben da za ayi a Ekiti ne kwamitin zai lura da yadda sauran zabukan 2023 za su kasance.

Yakin zaben Atiku

Ku na da labari alkawarin da Atiku Abubakar ya yi shi ne Gwamnatin Tarayya za ta cire hannunta a kan sha’anin matatun masu tace danyen mai.

Sannan ‘dan takarar zai bar wa ‘yan kasuwa kula da jirgin kasa da kamfanin wutar lantarki, kuma za a bar farashin komai ne a hannun ‘yan kasuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel