Yan Sanda Sun Nemi A Biya Su 'Allawus Na Siyan Kororon Roba' Yayin Da Suke Waka Da Rawa Gabanin Zaben Ekiti

Yan Sanda Sun Nemi A Biya Su 'Allawus Na Siyan Kororon Roba' Yayin Da Suke Waka Da Rawa Gabanin Zaben Ekiti

  • Wasu jami'an yan sanda da aka tura jihar Ekiti domin zaben gwamna na 2022 sun nuna alamun cewa a shirye suke su kare masu zabe
  • An kuma hangi yan sandan suna rawa da wakoki yayin da suke atisayensu na nuna shirinsu na kare mutane yayin zaben
  • Yayin atisayen, jami'an tsaron sun kuma nemi a basu kudaden allawus da za su siya kororon roba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wasu jami'an rundunar yan sandan Najeriya wanda aka tura su samar da tsaro a zaben gwamna da za a yi a ranar Asabar 18 ga watan Yuni a Jihar Ekiti sun gabatar da babban bukata.

Jami'an yan sandan yayin atisayen da suka yi na nuna shirinsu a hedkwatar rundunar yan sanda na Jihar Ekiti a Ado Ekiti sun nemi a basu allawus na siyan kororon roba, rahoton Legit.ng.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari: Sai mun rukurkusa duk masu cin gajiyar rashin tsaron kasar nan

Yan Sanda Suna Rawa Da Waka Gabanin Zaben Ekiti na 2022.
Yan Sanda Sun Nemi A Biya Su 'Allawus Din Siyan Kororon Roba' Yayin Da Suke Waka Da Rawa Gabanin Zaben Ekiti. Hoto: Hoto: Emmanuel Osodi.
Asali: Original

Kuma domin nuna cewa sun shirya tsaf domin kare rayuka da dukiyoyin a zaben gwamna na shekarar 2022 wanda za a yi kasa da awa 24, an hangi jami'an yan sandan suna rawa da wakoki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A yayin da suke rera wakoki daban-daban masu ban dariya, daya daga cikinsu ya bukaci a biya su allawus dinsu na kororon roba yayin bada amsa cikin nishadi.

An kuma hangi jirgi mai saukan ungulu da aka samar a jihar domin taimakawa yan sandan yana yawo kasa-kasa a sararin samaniya a babban birnin jihar.

Yan sandan wadanda suka fito daga sassa daban-daban na rundunar suna ta gudanar da harkokinsu cikin annashuwa yayin atisayen.

Zaben Gwamnan Ekiti: Mazauna Jihar Sun Bayyana Wadanda Za Su Zaba

A wani rahoton, gabanin zaben gwamnan Jihar Ekiti, mazauna jihar wadanda suka yi magana da Legit.ng sun bayyana yan takarar da suka fi so a cikin wadanda ke neman kujerar gwamnan jihar.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Hatsaniya Ta Barke a Hedkwatar APC Na Kasa, Matasa Na Yi Wa Adamu Barazana

Akwai yan takarar gwamna guda 16 da suka shiga takarar na neman gaje kujerar Gwamna Kayode Fayemi.

Wasu cikin yan takarar su ne: Oluwole Oluyede na African Democratic Congress (ADC); Kemi Elebute Halle na Action Democratic Party (ADP); Biodun Oyebanji na All Progressives Congress (APC); Olabisi Kolawole na Peoples Democratic Party (PDP); tsohon gwamna Segun Oni, na Social Democratic Party (SDP) da Ranti Ajayi daga Young Progressives Party (YPP).

Asali: Legit.ng

Online view pixel