2023: Jerin abubuwa 5 da su ka jawo Atiku ya ki daukar Wike, ya zabi Okowa a PDP

2023: Jerin abubuwa 5 da su ka jawo Atiku ya ki daukar Wike, ya zabi Okowa a PDP

  • Ifeanyi Okowa ne wanda Alhaji Atiku Abubakar ya zaba a matsayin abokin takararsa a Jam’iyyar PDP
  • An yi tunani Gwamna Nyesom Wike ne zai zama ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa a zaben 2023
  • Babu mamaki Atiku yana ganin Dr. Okowa zai fi dacewa da shi a kan tsohon abokin hamayyarsa

A wannan rahoto, Daily Trust ta kawo dalilan da ake zagin su ne suka jawo Atiku Abubakar ya dauki Dr Ifeanyi Okowa, a maimakon Nyesom Wike.

1. Yakin neman tikiti

Atiku Abubakar da Nyesom Wike sun gwabza wajen neman tikitin PDP na zaben 2023, inda Gwamnan ya nemi ya kawowa Wazirin Adamawa babbar barazana.

Nyesom Wike ya yi ta sukar wadanda suka bar PDP a 2014 a wajen kamfe da yake yi, ko da Atiku bai taba tanka shi ba, hakan ya nuna ‘yar tsamar da ke a tsakaninsu.

2. Dabi’ar Wike

Jaridar ta na zargin halayar Gwamnan na Ribas da irin dabi’arsa ta jawo Atiku Abubakar wanda ba mutum ba ne mai hayaniya, ya ki zaben shi a matsayin abokin takara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shi Wike mutum ne mai hayaniya da fadan duk abin da ya zo masa ba tare da jin wani tsoro ba. A gefe guda kuwa, Ifeanyi Okowa ya na yanayi da ‘dan takaran na PDP.

3. Kokari a zaben fitar da gwani

Legit.ng Hausa ta na zaton Sanata Okowa ya taka rawar gani wajen nasarar da Atiku Abubakar ya samu a zaben fitar da gwani, inda ya doke Nyesom Wike da wasunsa.

Sakayyar da Atiku zai yi wa Okowa shi ne ya dauke shi a matsayin mataimaki. Daukar Wike zai zama Okowa ya yi biyu babu a 2023 bayan ya yi fada da makwabacin na sa.

Gwamna Wike
Gwamna Wike da wasu 'Yan PDP a kamfe Hoto: www.pulse.ng
Asali: UGC

4. Atiku v Wike

Tun can dai babu jituwa sosai tsakanin Atiku Abubakar da Gwamna Wike. Rahoton ya ce a zaben fitar da gwani na 2019, Wike ya goyi bayan Aminu Tambuwal a kan Atiku.

Nyesom Wike bai kallon Atiku a matsayin abokin tafiya, sai ma wanda ya baro APC zuwa jam’iyyar PDP domin ya yi takara da shi bayan sun gama wahala da jam’iyya.

5. Kalaman Nyesom Wike

Wasu maganganun Wike za su iya zama matsala a gare shi. Da bakinsa ya taba nuna kiyayyarsa ga Atiku, kuma ya taba cewa bai sh’awar kujerar mataimakin shugaban kasa.

Haka zalika za a iya amfani da wasu babatun Gwamnan na jihar Ribas a yankin Arewacin Najeriya domin a kawowa takarar Atiku da PDP barazana a zaben mai zuwa.

Peter Obi matsalo ne - Mbaka

Ana da labari Fasto Ejike Mbaka wanda tun kafin a je ko ina ya gano Goodluck Jonathan zai fadi zaben 2015 yace a 2023, 'dan takarar LP, Peter Obi wahalar banza kurum zai yi.

Fasto Mbaka ya zargi Obi da cewa hannunsa a rufe suke domin ba ya kyauta, yace Atiku Abubakar ya huta da ya rabu da shi a zaben 2023 bayan sun yi takara tare a wancan karo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel