Jigon PDP Zai Yi 'Murabus' Saboda Atiku Ya Zabi Okowa a Matsayin Mataimakinsa, Ya Ce Zai Yiwa Tinubu Kamfen

Jigon PDP Zai Yi 'Murabus' Saboda Atiku Ya Zabi Okowa a Matsayin Mataimakinsa, Ya Ce Zai Yiwa Tinubu Kamfen

  • Kassim Afegbua, jigon jam'iyyar PDP a jihar Edo ya ce akwai alama zai raba jiha da PDP saboda zaben Okowa matsayin mataimakin Atiku a zaben 2023
  • Afegbua ya zargi Gwamna Okowa da cin amanar mutanen kudu, inda ya bawa Atiku kuri'u yayin zaben cikin gida don ya bashi takarar mataimaki
  • A cewar Afegbua, ba zai fita daga jam'iyyar PDP ba amma zai yi wa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu kamfen a maimakon jam'iyyarsa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Tsohon kwamishina na labarai a Jihar Edo, Kassim Afegbua, ya bada alama cewa za bar jam'iyyar PDP saboda zaben Gwamna Jihar Delta, Ifeanyi Okowa, a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa a zaben 2023, rahoton Premium Times.

Jam'iyyar na PDP a ranar Alhamis da rana ta gabatar da Mr Okowa a matsayin abokin takararsa a zaben da za a yi a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

Kara karanta wannan

Dalilin da Yasa na Darzo Okowa A Matsayin Abokin Takarata a 2023, Atiku Abubakar

Okowa da Afegbua
2023: Jigon PDP Zai Yi Murabus Saboda Atiku Ya Zabi Okowa a Matsayin Mataimakinsa. Hoto: @PremiumTimesNg.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Amma Mr Afegbua, wanda tsohon kakaki ne ga tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Ibrahim Babangida, ya ce Gwamnan Jihar Rivers Nyesom Wike, ya cancanci a zabe shi gabanin Mr Okowa.

Mr Wike ya zo na biyu a zaben cikin gida na shugaban kasa na jam'iyyar ta PDP inda Okowa ya jagoranci daligets dinsa suka zabi Atiku.

Okowa ya ci amanar yan kudu, ya bawa Atiku kuri'u don ya zabe shi mataimaki, Afegbua

Mr Afegbua ya bayyana zaben gwamnan Delta da Atiku ya yi a matsayin sakayya na cin amana, yana mai cewa Okowa ya kira taron gwamnonin kudu a Asaba a shekarar 2021 inda gwamnonin suka cimma matsayar shugaban kasa na gaba ya fito daga kudu.

Mr Afegbua ya yi magana ne a ranar Alhamis yayin shirin The Arise Interview.

Kara karanta wannan

Okowa: Muhimman abubuwa 12 da baku sani ba game da abokin takarar Atiku a PDP

A wani mataki na nuna rashin amincewa da cin amanar da Mr Okowa ya yi na goyon bayan Atiku a zaben fidda gwani don ya zabe shi matsayin mataimakinsa, Mr Afegbua ya ce zai janye goyon bayansa daga PDP kuma zai goyi bayan dan takarar APC, Bola Ahmed Tinubu a zaben 2023.

Mr Afegbua ya jadada cewa ba zai shiga APC ba amma zai rika yi wa dan takarar ta kamfen.

Tsohon kwamishinan ya taba juya wa PDP baya a 2020 saboda bawa Gwamna Godwin Obaseki tikitin tazarce bayan APC ta soke takararsa saboda zarginsa da gabatar da takardan karatu na karya.

Mr Obaseki daga bisani ya ci zaben gwamna a PDP a yayin da jam'iyyar ta dakatar da Mr Afegbua kan zargin yi mata zagon kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel