Tsohon gwamna ya saki jerin sunayen jiga-jigan APC da wasu mutane da basa son Bola Tinubu

Tsohon gwamna ya saki jerin sunayen jiga-jigan APC da wasu mutane da basa son Bola Tinubu

Gabannin zaben shugaban kasa na 2023, tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya bayyana cewa mutane da dama a cikin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki basa son dan takararsu na shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.

Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne a cikin wata hira da ya yi da jaridar Vanguard.

Tsohon gwamna ya saki jerin sunayen jiga-jigan APC da wasu mutane da basa son Bola Tinubu
Tsohon gwamna ya saki jerin sunayen jiga-jigan APC da wasu mutane da basa son Bola Tinubu Hoto: Megalcon Magazine
Asali: UGC

A cewarsa, wadannan rukunin mutanen basa kaunar Tinubu:

  1. Afenifere
  2. Gwamnonin APC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wadanda ba za su marawa takarar shugabancin Tinubu baya ba

  1. Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Ga abun da Lamido ya ce:

“Da kyau, idan yanzu gwamnonin kudu gaba daya suka ce duk za su koma APC, bari su fadi haka. Sannan sai a samu mutum kamar Amaechi a matsayin shugaban kasa, shin kuna ganin Wike zai yarda? Yanzu haka, Tinubu na shan gwagwarmaya daga wa? Yan uwansa! Afenifere basa son Tinubu kuma sun sha fadin haka a bayyane. Gwamnonin APC ma basa son Tinubu. Sun ce ya cika mamayewa kuma shi mai mulki kama karya ne. ina nufin shi dansu ne, mai zai hana su sa shi?

Kara karanta wannan

Na zabi Musulma matsayin mataimakiyar gwamna kuma babu abinda ya faru, El-Rufa'i

“Don haka, mu kasance masu gaskiya da amana a abun da muke yi. Idan kudancin Najeriya zasu hade sannan su ce “Muna son samar da shugaban kasa daga kudu, toh su rusa iyakar siyasarsu ta zama jam’iyyar siyasa daya sannan a ce, a misali, Amaechi ya zama dan takara, bana tunanin Wike zai yarda.
“Ku duba zancena, Buhari ba zai taba marawa Tinubu baya ba saboda tunanin mutumin. Ba zai taba marawa Tinubu baya ba. Mutane basu yarda dani ba kuma ku jira ku gani. A yanzu, gwamnonin APC sun hade ma Tinubu kai. Don haka batun samun namu kamar yadda kudu ke bukata…Gwamnonin APC ne farkon hadewa Tinubu.”

Karshen tika-tiki: Kakakin kungiyar kamfen din Tinubu ya bayyana daga yankin da abokin takararsa zai fito

A wani labarin, kakakin kungiyar kamfen din Bola Tinubu ya bayyana cewa gwamnonin jam’iyyar APC na da yancin zabawa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar abokin takara.

Kara karanta wannan

Burin 2023: Ajandoji 7 da Bola Tinubu ke da burin yiwa 'yan Najeriya idan ya gaji Buhari

Da yake zantawa da jaridar The Punch, Bayo Onanuga, kakakin kungiyar kamfen din ya bayyana cewa abokin takarar Tinubu zai fito ne daga kowani bangare na yankin arewa kuma zai iya kasancewa daga kowani addini.

Onuga ya ce zai iya fitowa daga arewa maso gabas, arewa ta tsakiya ko kuma arewa maso yamma, kamar yadda jarida The Cable ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel