Kwankwaso ne zai lashe zaben shugaban kasa na 2023, in ji wani malamin addini

Kwankwaso ne zai lashe zaben shugaban kasa na 2023, in ji wani malamin addini

  • Wani malamin addini, Prophet Iwu Jideogu Ogbu, ya yi hasashen cewa Rabiu Musa Kwankwaso na jam'iyyar NNPP ne zai lashe zaben 2023
  • Ogbu ya kuma bayyana cewa Allah ya kaddara tsohon gwamnan na jihar Kanon shine zai magance matsalolin da ke addabar kasar nan
  • Ya ce Allah ya fara nuna masa nasarar Kwankwaso ne tun a 2014 lokacin da ya nemi tikitin shugabancin kasar na APC tare da Buhari

Lagos - Shugaban kungiyar kare hakkin Kirista da Musulmi, Prophet Iwu Jideogu Ogbu, ya bayyana wanda zai lashe babban zaben 2023 mai zuwa.

A cewar Ogbu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso ne zai lashe babban zaben mai zuwa

Kwankwaso ne zai daga tutar jam’iyyar NNPP wacce ta shafe shekaru sama da 20 amma ba’a jinta bayan ya farfado da ita.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Kwankwaso ya bayyana manufofinsa, ya ce zai kawo karshen matsalolin Najeriya

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso
Kwankwaso ne zai lashe zaben shugaban kasa na 2023, in ji wani malamin addini Hoto: Leadership
Asali: UGC

Da yake zantawa da manema labarai a Lagas, malamin addinin ya ce koda dai bai hadu da Kwankwaso ba kafin ya yi wannan hasashe, Allah ya nuna masa cewa shine zai zama shugaban kasa na gaba, jaridar Leadership ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma bayyana cewa Allah ya kaddara dan takarar na NNPP ne zai magance matsaloli da dama da suka dabaibaiye kasar wadanda suka hada da rashin tsaro, tabarbarewar tattalin arziki, rabuwar kai da ke kara munana da kuma rashin jituwa ta addini a tsakanin al’ummar kasar.

Ya kuma kara da cewar shine zai kai ga cimma tsarin tarayya ta gaskiya da yan Najeriya da dama ke muradi.

Ya ce:

“Kafin na yi wannan hasashen, ban hadu da wannan mutumin da ake kira Kwankwaso ba. Karo na farko da Allah ya nuna hakan ya kasance a 2014 lokacin da shi (Kwankwaso) ya yi takarar tikitin shugaban kasa na APC tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar inda Buhari ya lashe tikitin jam’iyyar.”

Kara karanta wannan

Ka kusa zama Jagaban Najeriya - Babagana Kingibe ya fada ma Tinubu cewa shine zai dare kan kujerar Buhari

Kwankwaso: Ni zan magance matsalar rashin tsaro, na daidaita tsarin ilimi bayan mulkin APC

A gefe guda, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP Engr Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi alkawarin magance matsalar rashin tsaro da samar da ingantaccen ilimi a kasar idan ya zama shugaban kasa.

Tsohon ministan tsaro kuma gwamnan jihar Kano, ya kuma ce zai bullo da kyawawan manufofin tattalin arziki da za su ciyar da kasa gaba, Leadersip ta ruwaito.

Kwankwaso ya yi wannan alkawarin ne a jiya a lokacin da yake gabatar da jawabi a cibiyar Kolanut, a wata ganawa da wakilan jam’iyyar NNPP a Calabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel