Kwankwaso: Ni zan magance matsalar rashin tsaro, na daidaita tsarin ilimi bayan mulkin APC

Kwankwaso: Ni zan magance matsalar rashin tsaro, na daidaita tsarin ilimi bayan mulkin APC

  • Tsohon gwamnan Kano, kuma dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar NNPP mai kwandon kayan dadi ya bayyana manufarsa
  • Kwankwaso ya bayyana cewa, shi ne zai iya magance matsalar tsaro da Najeriya ke fuskanta a halin yanzu
  • Ya kuma ce, zai kawo karshen matsalolin da ke addabar ma'aikatar ilimi tare da inganta tattalin arziki

Calabar, Kiros Riba - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP Engr Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi alkawarin magance matsalar rashin tsaro da samar da ingantaccen ilimi a kasar idan ya zama shugaban kasa.

Tsohon ministan tsaro kuma gwamnan jihar Kano, ya kuma ce zai bullo da kyawawan manufofin tattalin arziki da za su ciyar da kasa gaba, Leadersip ta ruwaito.

Kwankwaso ya yi wannan alkawarin ne a jiya a lokacin da yake gabatar da jawabi a cibiyar Kolanut, a wata ganawa da wakilan jam’iyyar NNPP a Calabar.

Kara karanta wannan

Labari Mai Zafi: Masu Ruwa da Tsakin APC Sun Magantu Kan Tikitin Musulmi da Musulmi

Kwankwaso ya magantu kan manufofinsa
Kwankwaso: Ni zan iya magance matsalar rashin tsaro, na daidaita tsarin ilimi bayan 2023 | Hoto: sunnewsonline.com
Asali: UGC

Ya bayyana cewa zamansa a fadar shugaban kasa, rashin tsaro da ya addabi al’ummar kasar a ‘yan kwanakin nan, zai zama tarihi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ba da tabbacin samar da ingantaccen ilimi da ingantattun tsare-tsare na tattalin arziki da za su taimaka wajen raya arzikin kasa, inda ya yi kira ga ‘yan Najeriya na gida da na kasashen waje da su hada kai wajen zaben sa a matsayin shugaban kasa.

A kalaman Kwankwaso:

"Zan magance matsalar rashin tsaro, na samar da ilimi mai inganci da ingantattun tsare-tsare na tattalin arziki da za su iya daga al'ummar kasar zuwa kan tudun mun tsira."

A jawabinsa na farko shugaban NNPP na jihar Kuros Riba, Tony Odey, ya bayyana cewa zaman Kwankwaso a kan kujerar shugaban kasa, matsalar rashin tsaro za ta zama tarihi.

Kara karanta wannan

Burin Atiku a zaben 2023: Ina sa ran 'yan Najeriya za su yi kasa-kasa da jam'iyyar APC

Kwankwaso ne mafita, inji jigon siyasa

Ya kuma bukaci kowa da kowa ya tashi tsaye domin ganin Kwankwaso ya zama shugaban kasa, inji Daily Sun.

A cewarsa:

“Najeriya za ta samu idan aka zabi Kwankwaso. Duk da cewa an mayar da Siyasar Najeriya ta zama wasa da daloli, mun samu wani fitaccen mai gina kasa, wato Engr. Rabiu Kwankwso.
“Kwankwso ya zo da kwarin gwiwar da muka cancanta.
"Najeriya na muradin ganin sauyi kuma mutum daya tilo da zai iya haifar da wannan sauyi shine Kwankwaso."
“Ya yi yaki da rashin tsaro a lokacin da yake mulki a matsayin gwamnan jihar Kano ba tare da zubar da jini ba. Ina ganin idan muka ba shi dama zai iya yin irin haka a shugabancin Najeriya.”

Malamin addini: Ba a taba mulkin 'yan rashawa kamar na Buhari ba a tarihin Najeriya

A wani labarin, shugaban cocin Living Faith Church Worldwide, Bishop David Oyedepo, ya caccaki gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ya bayyana ta a matsayin wadda tafi kowacce cin hanci da rashawa a tarihin Najeriya.

Kara karanta wannan

Babban karramawar da za a yiwa jaruman damokradiyya shine fatattakar APC daga mulki – Atiku Abubakar

Da yake jawabi a wani shiri na baya-bayan nan a cocin sa, Oyedepo ya koka da irin halin kuncin da kasar ke ciki, inda ya danganta hakan da cin hanci da rashawa, Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce Naira biliyan 80 da ake zargin Akanta-Janar na Tarayya, Ahmed Idris ya sace, za su isa su biya bukatun kungiyar Malaman Jami’o’i, ASUU, wanda ya kai ga rufe makarantu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel