Labari Mai Zafi: Masu Ruwa da Tsakin APC Sun Magantu Kan Tikitin Musulmi da Musulmi

Labari Mai Zafi: Masu Ruwa da Tsakin APC Sun Magantu Kan Tikitin Musulmi da Musulmi

  • Kungiyar masu ruwa tsakin jam'iyyar APC ta ce kada jam'iyyar ta yi kuskuren yin tikitin Musulmi da Musulmi a kasar nan
  • Shugaban Kungiyar, Aliyu Audu, ya sanar da cewa yin hakan zai matukar raba kan talakawa kuma zai tabbatar da rashin zaman lafiya
  • Ya kara da bayyana cewa, jam'iyyar kada ta yi kuskuren, domin shugaba nagari zai iya zama Musulmi ko Kirista

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Masu ruwa da tsakin jam'iyyar APC sun yi kira ga shugabancin jam'iyyar da Kungiyar Progressive Governors da su tsaya neman mataimakin 'dan takarar shugabancin kasa kan Kiristocin arewa.

Punch ta ruwaito cewa, damuwarsu tana da tushe ne bayan cece-kuce ya yi yawa kan tikitin Musulmi da Musulmi wanda ya janyo maganganu daban-daban a kwanakin da suka gabata.

Shugaba Buhari, Bola Tinubu da Abdullahi Adamu yayin mika wa Tinubu tutar jam'iyya
Labari Mai Zafi: Masu Ruwa da Tsakin APC Sun Magantu Kan Tikitin Musulmi da Musulmi. Hoto daga Punchng.com
Asali: UGC

A yayin jawabi a wani shiri na shagalin bikin ranar damokaradiyya, Shugaban Kungiyar masu ruwa da tsakin APC na kasa, Aliyu Audu, ya bayyana bukatar watsi da duk wani abu da zai sa a dauko mataimaki Musulmi domin tabbatar da cigaban hadin kan kasar nan.

Kara karanta wannan

2023: CAN ta Aike Sako ga Masu Neman Shugabancin Kasa, Ta Sanar da Irin 'Dan Takarar da Zata Zaba

Ya ce, "Dalilin da yasa muka ankare da cewa kada addini ya zama madogara wurin zaben shugaba. Halin da kasar nan ta tsinci kanta a ciki yasa muka yanke wannan shawarar, matukar sun damu da rayukanmu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A yau, kasar mu ta rabe a bangaren kabilanci da addini kuma ba za mu iya zuba ido a wannan abu mai muhimmanci ba.
"Wannan ne dalilin da yasa muke tunanin dole a saka APC a hanya yayin zaben mataimakin 'dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar.

Audu ya ce, kin bin wannan shawarar zai assasa wutar rabuwar kan talakawa kuma ya kawo rabewar kai.

Kamar yadda yace, Najeriya tana bukatar shugabanci nagari, wanda zai iya zuwa daga shugaba Musulmi ko Kirista.

2023: CAN ta Aike Sako ga Masu Neman Shugabancin Kasa, Ta Sanar da Irin 'Dan Takarar da Zata Zaba

Kara karanta wannan

Babban karramawar da za a yiwa jaruman damokradiyya shine fatattakar APC daga mulki – Atiku Abubakar

A wani labari na daban, Kungiyar Kiristoci ta Kasa, CAN, ta ce duk jam'iyyar siyasa da ke son cin zaben shugabancin kasa a 2023 dole ne ta hada kai da coci.

Samson Ayokunle, shugaban CAN, ya sanar da hakan a ranar Lahadi yayin jawabin bikin ranar damokaradiyya na 2022 wanda aka yi a Cibiyar Kiristoci ta Kasa da ke Abuja, The Cable ta ruwaito.

Ayokunle wanda ya samu wakilcin Wale-Oke, shugaban Pentecostal Fellowship of Nigeria, ya ce duk jam'iyyar da ke son samar da shugaban kasa na gaba dole ne ta hada kai da yankunan Kiristoci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel