2023: Wasu Matasa Biyu Sunyi Tafiyar Kilo Mita 205 Don Dan Takarar Gwamnan Bauchi

2023: Wasu Matasa Biyu Sunyi Tafiyar Kilo Mita 205 Don Dan Takarar Gwamnan Bauchi

  • Wasu matasa sun su biyu sun taka daga Azare zuwa a karamar hukumar Katagum zuwa Bauchi don taya dan takarar gwamnan APC na Bauchi murna
  • Abu Samaila da Abubakar Yusuf sun ce sun yi wannan tattakin ne don murna da nuna kauna ga dan takarar gwamnan na APC, Air Marshal Abubakar Saddique
  • Shugaban kungiyar yakin neman zaben Air Marshal Abubakar Saddique ta tarbi matasan biyu tana mai cewa abin da suka yi abin yaba wa ne kuma ya gode musu

Jihar Bauchi - Wasu matasa sun yi tafiyar kilo mita 205 domin nuna goyon baya ga dan takarar gwamna na jam'iyyar APC a jihar Bauchi, Air Marshal Saddique Abubakar (mai ritaya).

Kamfanin dillancin labarai (NAN) ta rahoto cewa wasu matasa, Abu Samaila, 35, da Abubakar Yusuf, 25, sun yi tafiya daga Azare a karamar hukumar Katagum na Jihar Bauchi zuwa babban birnin jihar, cikin kwana uku.

Kara karanta wannan

2023: Dalilin da Yasa APC ta Zabi Tinubu, El-Rufai Ya yi Bayani Mai Bada Mamaki

2023: Wasu Maza Biyu Sunyi Tafiyar Kilo Mita 205 Don Dan Takarar Gwamnan Bauchi
2023: Matasa Biyu Sunyi Tafiyar Kilo Mita 205 Don Dan Takarar Gwamnan Bauchi. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Matasan biyu sun shaida wa NAN a ranar Lahadi a Bauchi sun yi tattakin ne don murnar nasarar da Abubakar ya yi a zaben fidda gwani na APC a Bauchi a da aka yi a baya-bayan nan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abubakar, tsohon babban hafsan sojojin saman Najeriya ya kayar da yan takara bakwai ya yi nasarar samun tikitin, Daily Trust ta rahoto.

A cewar matasan, tattakin da suka yi na cikin soyayyar da suke yi wa Abubakar da kuma godiya bisa gudunmawar da ya bada a baya wurin cigaban kasa.

Sun yi bayanin cewa ra'ayinsu ne yin tattakin ba tare da sun tuntubi wani ba ko sanar da niyyarsu.

Matasan biyu sun ce Abubakar ya yi wa jihar da kasar hidima sosai, ya kara da cewa ya kawo cigaba sosai ga jihar don haka ya cancanci yabon.

Kara karanta wannan

2023: Jam'iyyar ADC Ta Zabi Dan Takarar Shuagban Kasa, Ya Yi Alkawarin Yi Wa Tinubu Da Atiku Ritaya

"A kan hanyar mu, mun wayar da kan daruruwan matasa su taya mu yi wa Abubakar kamfen na inganta Bauchi karkashin Abubakar a matsayin gwamna.
"Mun yi imanin cewa shi kadai zai iya magance matsalar rashin aikin yi, fatara, rashin tsaro da wasu kallubale da ke adabar jihar," in ji Samaila.

A cewar Yahaya, sun baro Azare misalin karfe 6.30 na safiyar Litinin kuma suka iso Bauchi a ranar Alhamis.

Shugaban kungiyar kamfen din Abubakar ta tarbi matasan

Mr Yahaya Miya, shugaban kungiyar yakin neman zaben Air Marshal Abubakar ya yaba wa matasan biyu a wurin wani taro da aka yi don gode musu saboda goyon bayan Abubakar.

Ya gode wa matasan biyu bisa nuna goyon bayansu, soyayya da kauna ga dan takarar gwamna na jam'iyyar APC.

"Tattakin da suka yi, matasan sun nuna kishin kasa da goyon baya, ya kamata a gode musu kuma a karfafa musu gwiwa.
"Da isowarsu a ranar Alhamis, an fara kai su asibiti don duba lafiyarsu kuma suka huta na tsawon awa shida kafin aka kai su masaukinsu," in ji shi.

Kara karanta wannan

2023: Tambuwal Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Gwamnonin PDP Suka Yi Taro Da Atiku

"Muna godiya sosai bisa goyon baya," Miya ya ce a madadin dan takarar gwamnan na APC da jam'iyyar.

2023: Jerin Wadanda Ake Ganin Tinubu Zai Iya Dauka A Matsayin Mataimakansa

Kwanaki kadan bayan cin zaben fidda gwani da ya bashi damar zama dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC a 2023, Bola Tinubu na da wani aiki a gabansa na zaben mataimakinsa.

Sai dai dole sai an yi la'akari da abubuwa masu yawa wurin zaben abokin takarar Tinubu kuma dola jam'iyyar mai mulki ta mayar da hankali wurin zaben don hakan na iya zama dalilin cin zabe ko akasin haka.

Don haka, Legit.ng a wannan rahoton za ta yi nazari kan wasu daga cikin sunayen da aka hasashen za su iya zama mataimaka ga Asiwaju Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164