2023: Dalilin da Yasa APC ta Zabi Tinubu, El-Rufai Ya yi Bayani Mai Bada Mamaki

2023: Dalilin da Yasa APC ta Zabi Tinubu, El-Rufai Ya yi Bayani Mai Bada Mamaki

  • Gwamnan jihar Kaduna ya yi bayani game da dalilin da yasa jam'iyyar APC ta zabi Asiwaju Bola Tinubu domin takarar shugabancin kasa a 2023
  • A tattaunawar da aka yi da El-Rufai, ya bayyana cewa gwamnonin APC daga shiyyar arewa maso yamma sun aminta da Tinubu saboda ya fi kowanne 'dan takara kasuwa
  • Fitaccen 'dan siyasan ya sanar da yadda shugaba Buhari ya tsaya tsayin daka ba tare da ya zabi 'dan takarar da ya fi so ba daga cikin masu neman tikitin

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna a ranar Juma'a, 10 ga Yuni, ya bada bayanin yadda tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu, ya zama 'dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar APC.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa, ya caccaki wadanda suke sukar tikitin takara na musulmi da kuma mataimaki musulmi inda ya kwatanta su da wadanda ba su san abinda su ke yi ba.

Kara karanta wannan

Ba sauran hamayya: Yahaya Bello ya ba da tallafi mai tsoka ga ci gaban kamfen din Tinubu

2023: Dalilin da Yasa APC ta Zabi Tinubu, El-Rufai Ya yi Bayani Mai Bada Mamaki
2023: Dalilin da Yasa APC ta Zabi Tinubu, El-Rufai Ya yi Bayani Mai Bada Mamaki. Hoto daga Buhari Sallau
Asali: Facebook

Tinubu ya samu kuri'u 1,271 inda ya lallasa 'yan takara 13 a zaben fidda gwanin jam'iyyar APC da aka kammala a ranar Laraba, 8 ga watan Yuni.

El-Rufai ya bayyana dalilin da yasa aka zabi Tinubu

A yayin bayyana abubuwan da suka sa Tinubu ya tabbata 'dan takarar APC a zaben 2023 mai gabatowa, El-Rufai ya ce gwamnonin arewa maso yamma sun gana kafin zaben fidda gwanin kuma sun yanke hukuncin goyon bayan Tinubu saboda shi ne 'dan takara da yafi kowanne farin jini da masoya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Najeriya ta Dawo Hayyacinta, Za mu batar da Makasan Jama'a, Tinubu Ya Sha Alwashi

A wani labari na daban, 'dan takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar APC, Asiwaju Bola, ya tabbatar wa da 'yan Najeriya cewa zai yi duk abinda ya dace kuma daidai karfinsa wurin dawo da kasar nan hayyacinta tare da magance matsalar kashe-kashe.

Kara karanta wannan

An yi zalunci: Tawagar Yahaya Bello ta caccaki shugabannin APC bisa zaban Tinubu

Tinubu yayin mika jawabin nasarar da ya samu, bayan an bayyana shi a matsayin wanda ya ci zaben fidda gwani, ya ce kashe juna ba ya daga cikin cigaba, Vanguard ta ruwaito.

Ya ce, "Kauna tana nufin rungumar juna ne. Mu amince da cewa za mu gina kasa. Babu addinin da zai batar da wani a kasar."

Asali: Legit.ng

Online view pixel