2023: Jerin Wadanda Ake Ganin Tinubu Zai Iya Dauka A Matsayin Mataimakansa

2023: Jerin Wadanda Ake Ganin Tinubu Zai Iya Dauka A Matsayin Mataimakansa

  • Jam'iyyar APC mai mulki a kasa na da babban aiki a gabanta na zaben abokin takara ga Ahmed Bola Tinubu
  • An yi ta hasashen ana wallafa jerin sunan wasu mutane a kafafen watsa labarai kuma abi daya shine dukkan sunayen mutane ne daga arewa
  • Bisa ga dukkan alamu ba za a zabi dan kudu ba ko kudu maso kudu kuma bisa alamu Tinubu ba zai zabi musulmi ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kwanaki kadan bayan cin zaben fidda gwani da ya bashi damar zama dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC a 2023, Bola Tinubu na da wani aiki a gabansa na zaben mataimakinsa.

Sai dai dole sai an yi la'akari da abubuwa masu yawa wurin zaben abokin takarar Tinubu kuma dola jam'iyyar mai mulki ta mayar da hankali wurin zaben don hakan na iya zama dalilin cin zabe ko akasin haka.

Kara karanta wannan

Takarar Musulmi da musulmi: Ana yiwa Tinubu zagon kasa ne, in ji wani fasto

2023: Jerin Wadanda Tinubu Zai Iya Dauka a Matsayin Mataimakansa
Jerin wadanda ake ganin Tinubu zai iya dauka a matsayin mataimakansa. Hoto: @NGRPresidency.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Don haka, Legit.ng a wannan rahoton za ta yi nazari kan wasu daga cikin sunayen da aka hasashen za su iya zama mataimaka ga Asiwaju Bola Tinubu.

1. Babagana Zulum (Borno)

Sunansa na cigaba da fitowa da bakunan masu nazarin harkokin siyasa da magoya baya.

Gabanin zaben fidda gwani na shugaban kasa a APC, Legit.ng ta rahoto cewa kungiyoyin siyasa da masu nazari sun yi hasashen cewa tikitin shugaban kasa na Osibajo/Zulum.

Amma, wani rahoton na Legit.ng ta wallafa, Gwamnan na Borno jim kadan bayan samun nasarar lashe tikitin takarar gwamna ya ce bashi da sha'awar yin takarar shugaban kasa ko kuma mataimaki a APC.

Ya ce abin da ke gabansa shine karasa ayyukan da ya fara shekaru uku da suka gabata kuma shi mutanen Borno ya ke son yi wa hidima.

Kara karanta wannan

Burin 2023: Ajandoji 7 da Bola Tinubu ke da burin yiwa 'yan Najeriya idan ya gaji Buhari

Amma, ko da Zulum sai canja shawara, kasancewar shi da Tinubu dukkansu musulmi ne ka iya zama cikas, da dai Osinbajo ne ya ci takarar shugaban kasa a APC ko Rotimi Amaechi da Zulum zai dace matuka.

2. Nasir El-Rufai (Kaduna)

Gwamnan Jihar Kadunan ya yi fice wurin ayyukan raya gari da gine-gine musamman a lokacin da ya yi minista a Abuja.

Amma, El-Rufai musulmi ne don haka tsayar da musulmi da musulmi takara zai iya zama matsala ga jam'iyyar, don haka da wuya a zabe shi a matsayin mataimaki.

3. Samuel Lalong (Plateau)

Bisa la'akari da al'adar da aka saba na tsayar da musulmi da kirista, Gwamnan na Plateau, Samuel Lalong ka iya zama cike gurbin mataimakin Tinubu.

Amma, akwai wani abu guda daya da zai iya zama masa cikas wurin zabensa a matsayin mataimaki.

A cewar wani rahoto da Vanguard ta wallafa, akwai jita-jita da ke yawo cewa daligets din jiharsa ba su zabe Bola Tinubu ba.

Kara karanta wannan

Manyan dalilai 4 da suka sa Tinubu ya lashe tikitin shugaban kasa na APC

4. Honarabul Yakubu Dogara

Zaben Yakubu Dogara ba zama wani matsala ba domin kasancewarsa kirista kamar Lalong, gwamnan Jihar Plateau.

Amma, Legit.ng ta fahimci cewa alakar tsohon kakakin majalisar wakilai na tarayyar da babban jam'iyyar hamayya wato PDP ka iya zama cikas wurin zabensa don cike wannan gurbin.

5. Boss Mustapha, Sakataren Gwamnatin Tarayya

Bisa dukkan alamu yana daya daga cikin mutanen da ka iya zama abokan takarar Tinubu idan aka yi la'akari da yankin da ya fito da kuma addininsa, ya kuma cancanci wannan matsayi na mataimakin shugaban kasa.

Buratai: Tsohon Babban Hafsan Sojojin Ƙasan Najeriya Ya Ba Wa APC Gudunmawar Motar Kamfen Ƙirar Najeriya

A wani rahoton, tsohon babban hafsan sojin kasa kuma Jakadan Najeriya a Jamhuriyar Benin, Janar Tukur Buratai; Babban Kwamishinan Najeriya a Jamhuriyar Zambia, Nwanebike Oghi da kuma wasu jakadu na musamman a ranar Laraba sun bai wa shugabancin jam’iyyar APC kyautar motoci kirar bas mai daukar mutum 18.

Kara karanta wannan

Tinubu zai shiga farautar Mataimakinsa gadan-gadan, watakila a tsaida Gwamna mai-ci

Farar motar, wacce kamfanin Innoson Motors ne ya kerata sabuwa ce kuma a jikinta a rubuta “Jakadu na musamman ne su ka bayar da kyautarta,” The Punch ta ruwaito.

Sun gabatar da motar ne a babban ofishin jam’iyyar da ke Abuja bayan wakilan sun yi taron sirri da shugaban jam’iyyar, Sanata Abdullahi Adamu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164