Tinubu ya mamayi Farfesa Osinbajo, ya kai masa ziyara kwatsam har ofishinsa a Aso Villa

Tinubu ya mamayi Farfesa Osinbajo, ya kai masa ziyara kwatsam har ofishinsa a Aso Villa

  • An yi matukar mamakin ganin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a ofishin mataimakin shugaban Najeriya
  • ‘Dan takarar shugaban kasan na APC ya je wajen Yemi Osinbajo jiya ba tare da an san da zuwansa ba
  • Bola Tinubu da mutanensa sun hadu da Osinbajo ne jim kadan bayan ya taya shi murnar samun takara

Abuja - ‘Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zabe mai zuwa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya kai wa Farfesa Yemi Osinbajo ziyara a jiya.

Kamar yadda mu ka samu labari daga Hadimin gwamnan Legas, Jibril Gawat a shafinsa na Twitter, babu wanda ya san da labarin wannan ziyara.

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci Mai girma mataimakin shugaban kasar ne a ranar Alhamis ba tare da ya sanar da kowa kan zuwansa ba.

Kara karanta wannan

Zaben APC: Yadda Gwamnoni, Jagororin Arewa da ‘Yan NWC suka ba Bola Tinubu nasara

Sanarwar ta ce ‘dan takaran na APC ya hadu da Yemi Osinbajo a gidansa da ke Aguda House a fadar shugaban Najeriya da ke birnin tarayya Abuja.

Ana zaune sai ga Jagaban

Wata majiya a fadar shugaban kasar ta bayyanawa Premium Times cewa su na zaune ne kurum sai suka ji labarin Tinubu ya iso gidan Yemi Osinbajo.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiyar ta ce tsohon gwamnan na jihar Legas ya rika yin wasa da raha, yana bada labarin irin gudumuwar da Osinbajo ya bada a tafiyar siyasarsa.

Asiwaju Tinubu da VP
Bola Tinubu da Farfesa Osinbajo Hoto: @Mr_JAGs
Asali: Twitter
“Mu na zaune ne kurum, sai aka sanar da mataimakin shugaban kasa cewa Asiwaju ya iso.”

- Majiyar

Tinubu ya yi bayani musamman a kan kokarin da Farfesa Osinbajo ya yi wajen nemawa tsohuwar jam’iyyarsu ta ACN nasara a kotu a zaben jihar Osun.

Kara karanta wannan

Manyan dalilai 4 da suka sa Tinubu ya lashe tikitin shugaban kasa na APC

Rahoton yake cewa Tinubu ya tuna da yadda mataimakin shugaban kasar ya je Ingila ana matsanancin sanyi domin ya kare jam’iyyarsu a gaban kotu.

Osinbajo ya yi amfani da fasahar zanen hannu domin gamsar da Alkali a shari’ar zaben gwamnan.

Mun zama 'yanuwa da Osinbajo

An ji Bola Tinubu yana cewa ya yi mamakin yadda wasu ke tunanin takarar da Osinbajo ya shiga a APC za ta shiga tsakaninsa da mataimakin shugaban kasar.

‘Dan takaran na APC ya fadawa mutanensa a yayin ziyarar shi da Farfesa Osinbajo sun zama tamkar ‘yanuwa, kuma yin takaran tikiti da shi ba laifi ba ne.

Hadarin motar 'yan APC

Dazu an samu labari Bola Tinubu ya fitar da jawabi ta bakin Bayo Onanuga, yana mai ta’aziyyar rashin da APC ta yi a reshen jihar Ribas na Onimiteim Samuel.

Marigayi Samuel ya kasance Sakataren jam’iyyar APC na karamar hukumar Akukutoru a Ribas kafin hadarin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa a hanyar Abuja.

Kara karanta wannan

Jerin mutane 6 da suka marawa Yemi Osinbajo baya akan Bola Tinubu

Asali: Legit.ng

Online view pixel