Motar da ta dauko ‘Ya ‘yan APC na Ribas tayi hadari, Sakataren jam’iyya ya mutu

Motar da ta dauko ‘Ya ‘yan APC na Ribas tayi hadari, Sakataren jam’iyya ya mutu

  • An samu karin bayani a game da hadarin da wasu ‘yan jam’iyyar APC suka yi a kan hanyar Abuja
  • Onimiteim Samuel ya mutu a sanadiyyar hadarin, wasu mutane bakwai kuma su na gadon asibiti
  • Marigayi Samuel shi ne Sakataren jam’iyyar APC na karamar hukumar Akukutoru a jihar Ribas

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Mutum daya aka samu labarin ya rasu a lokacin da wata motar Toyota Sienna da ke dauke da ‘ya ‘yan jam’iyyar APC suka yi hadari a Abuja.

Rahoton da Punch ta fitar ya ce wannan mota da za ta kai ‘yan jam’iyyar APC na jihar Ribas daga Abuja zuwa garin Fatakwal ta samu hadari ne a jiya.

Wani daga cikin wadanda suke motar, Innocent Amadi ya shaidawa jama’a haka da aka zanta da shi a gidan rediyon Nigeria Info news da ke Fatakwal.

Kara karanta wannan

Taron APC: Deliget din Rivers sun yi hatsari, mutum daya ya mutu

Innocent Amadi ya ce hadarin ya auku da kimanin karfe 8:00 na safiyar ranar Alhamis a kusa da rukunin gidajen jami’ar tarayya na Abuja a Gwagwalada.

Kamar yadda wannan mutumi ya bada labari, direbansu yana tsula gudu ne sai ya ci karo da wata mota a gabansa, don haka ya taka burki sosai nan-take.

A dalilin haka motar ta fadi, mutanen da ke cikin ta suka samu rauni. Ana jinyar wadannan mutane a asibitin koyar da aiki na jami’ar ta garin Abuja.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Titin Abuja
Wani titi a garin Abuja Hoto: www.julius-berger.com
Asali: UGC

Innocent Amadi ya tsira

A cewar Amadi, sai da motarsu ta juya a titi, amma shi kuwa ya tsira ba tare da ko kwarzane ba.

Ko da Allah ya yi masa gyadar doguwa, an rasa mutum daya a hadarin, sauran mutane bakwai kuma su na kwance a asibitin koyar da aiki na Abuja.

Kara karanta wannan

An yi zalunci: Tawagar Yahaya Bello ta caccaki shugabannin APC bisa zaban Tinubu

“Motarmu ta na gudu sosai. A sakamakon haka sai ga wata mota a kusa da shi.”
“Direban ya na matukar tsula gudu, bai iya rike motar ba. Sai ya taka burki, tayoyin suka cije.”
“Motar ta yi kundumbala. Ina kujerar gaba a motar. Na fito ban samu ciwo ba. Na daure kai na da igiyar kujera. Amma mun rasa mutum daya.”

- Innocent Amadi

Bola Tinubu ya fitar da jawabi ta bakin Darektan yada labaransa, Bayo Onanuga, yana mai ta’aziyyar rashin da APC ta yi a Akukutoru na Onimiteim Samuel.

Asali: Legit.ng

Online view pixel