Abubuwa 11 da baku sani ba game da Tinubu, dan takarar shugaban kasa na APC a 2023
Babban jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, shine ya zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a babban zaben 2023.
Ana daukar Tinubu a matsayin dattijo mai kishin kasa kuma dan Afrika da ya zamo madubin dubawa ga matasan nahiyar Afrika.
Ga wasu abubuwa da ya kamata ku sani game da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC.
1. An haife shi sannan an rada masa suna da Adekunle Bola Ahmed Tinubu a ranar 29 ga watan Maris, 1952 a jihar Lagas, da ke Najeriya.
2. Ya halarci makarantar Firamare na St. John, Aroloya Lagos da makarantar Children’s Home da ke Ibadan. Daga nan sai Tinubu ya tafi Amurka a 1975 inda ya fara karatu a kwalejin Richard J. Daley da ke Chicago, Illinois,sannan ya kuma je jami’ar Chicago.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
3. Ya mallaki kwalin digiri a fannin lissafin kudi daga jami’ar Chicago.
4. Saboda kwazonsa, an bashi lambar yabo mafi daraja bayan ya samu maki 3.54 cikin 4.0.
5. Da nasarorin da ya samu a fannin ilimi, matashin Tinubu ya tsaya takara kuma ya lashe zabensa na farko a siyasa a matsayin shugaban kungiyar lissafin kudi na makarantar a shekararsa ta karshe a jami’a.
6. Ya yi aiki da kamfanin Arthur Anderson, Deloitte and Sells da kuma GTE Services Corporation. Ya koma kamfanin Mobil Oil, Nigeria a 1983 bayan ya dawo Najeriya.
7. Ya rike sarautar Asiwaju na Lagas da kuma Jagaban na masarautar Borgu da ke jihar Neja.
8. A tsawon shekaru 8 da ya yi yana mulki a matsayin gwamnan Lagas, ya zuba jari mafi girma a bangaren ilimi sannan ya mayar da makarantu da dama ga ainahin masu shi.
9. Allah ya azurta shi da yara uku: Oluwaseyi Tinubu, Abibat Tinubu da Folashade Tinubu.
10. A ranar 28 ga watan Maris, 2021, Tinubu ya ziyarci sarkin Kano, a kokarinsa na hada kan kasa don ci gaba.
11. A ranar 8 ga watan Yuni, ya kayar da tsohon dansa a harkar siyasar, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo wajen zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki gabannin babban zaben 2023.
Asali: Legit.ng