Jerin mutane 6 da suka marawa Yemi Osinbajo baya akan Bola Tinubu

Jerin mutane 6 da suka marawa Yemi Osinbajo baya akan Bola Tinubu

Tsohon gwamnan jihar Lagas, Bola Ahmed Tinubu ya lallasa duk sauran yan takara, musamman tsohon dansa a fannin siyasa, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, wajen zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

An gudanar da zaben fidda dan takarar ne a filin Eagle Square da ke babbar birnin tarayya Abuja.

Ku tuna cewa a 2017, Yemi Osinbajo ya ce bai taba haduwa da Bola Tinubu ba lokacin da ya nada shi a matsayin Atoni Janar kuma kwamishinan shari’a a jihar Lagas a lokacin mulkinsa.

Jerin mutane 6 da suka marawa Yemi Osinbajo baya akan Bola Tinubu
Jerin mutane 6 da suka marawa Yemi Osinbajo baya akan Bola Tinubu Hoto: Sola Ade
Asali: Twitter

Hakazalika, a 2015, Tinubu ya ba dan takarar shugaban kasa na APC a wancan lokacin, Muhammadu Buhari shawarar daukar Osinbajo domin ya zama abokin takararsa.

Wasu mutane sun yi ikirarin cewa bai kamata Osinbajo ya yi takara da ubangidan nasa ba, amma wasu masu biyayya da goyon bayan mataimakin shugaban kasar basu aminta da su ba.

Kara karanta wannan

Yanzu: Atiku Da Gwamnonin PDP Sun Shiga Taron Sirri Bayan Nasarar Tinubu A Zaben Fidda Gwanin APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma, bayan an kammala shirin, Tinubu ne ya yi nasara sannan Legit.ng ta lissafo jerin sunayen mutanen da suka marawa mataimakin shugaban kasar baya akan tsohon ubangidan nasa.

1. Richard Akinnola

2. Tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola

3. Farfesa Sola Adeyeye

4. Babafemi Ojudu

5. Laolu Akande

6. Tsohon kwamishinan harkokin cikin gida na jihar Lagas, Abdul-Latest Abdul-Hakeem, wanda aka fi sani da Hon. Yeepe.

Atiku Abubakar ya taya Bola Tinubu murnar lashe tikitin APC

A gefe guda, mun ji cewa Ɗan takarar shugaban ƙasa da jam'iyyar PDP ta tsayar, Alhaji Atiku Abubakar, ya taya jagoran APC na ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, murnar samun nasara.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya ta ya Tinubu murnan ne a wani rubutu da ya yi shafinsa na dandanlin sada zumunta Tuwita.

Kara karanta wannan

Muhimman Dalilai 4 da suka sa Osinbajo ya Sha Mugun Kaye a Zaben Fidda Gwani

Tinubu, ya lashe zaɓen fidda ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC bayan shafe kwanaki ana gudanar da babban taron APC na musamman a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel