Babu daga kafa: Tinubu ya bayyana abin da zai yiwa PDP a zaben 2023

Babu daga kafa: Tinubu ya bayyana abin da zai yiwa PDP a zaben 2023

  • Jim kadan bayan tsallakewa a zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC mai mulkin kasar nan, Tinubu ya magantu
  • Ya bayyana shirinsa, inda yace dole ne jam'iyyar ta tsaya tsayin daka domin fatattakar jam'iyyar adawa ta PDP
  • Ya kuma nemi goyon bayan 'yan Najeriya da kuma 'yan jam'iyyar ta APC domin cimma wannan buri nasa na mulkar Najeriya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Jigo a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya zama dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar, rahoton Vanguard.

A yanzu dai Tinubu ne zai gwabza da dan takarar babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Alhaji Atiku Abubakar a babban zaben 2023 mai zuwa.

Martanin Tinubu ga 'yan PDP
Babu daga kafa: Tinubu ya bayyana abin da zai yiwa PDP a zaben 2023 | Hoto: punchng.com
Asali: Depositphotos

Tsohon gwamnan na Legas ya ce lokaci ya yi da APC za ta fatattaki jam’iyyar PDP da ya zarga da janyo wa al’ummar kasar koma baya.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Malik Ado-Ibrahim ya lashe tikitin takarar a YPP ta su Adamu Garba

A kalamansa na karbar nasarar, Tinubu ya caccaki PDP, inda yace babu abin da jam'iyyar ta jawowa Najeriya illa talauci da rayuwar kunci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakazalika, a kalamansa ya nemi goyon bayan dukkan 'yan jam'iyya da kuma ilahirin 'yan Najeriya domin kawo shugabanci nagari da ciyar da Najeriya gaba a zaben 2023.

Tinubu dai ya samu nasara ne da kuri’u 1,271 inda ya kayar da babban abokin hamayyarsa, Hon. Chibuike Rotimi Amaechi wanda ya samu kuri'u 316, kamar yadda Punch ta ruwaito.

A baya mun kawo muku rahoton da ke bayyana sunayen 'yan takarar da kuma adadin kuri'un da suka samu a wannan muhimmin zabe.

Atiku Abubakar ya taya Bola Tinubu murnar lashe tikitin APC

A wani labarin na daban, dan takarar shugaban ƙasa da jam'iyyar PDP ta tsayar, Alhaji Atiku Abubakar, ya taya jagoran APC na ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, murnar samun nasara.

Kara karanta wannan

Kebbi: Shugaban masu rinjaye a majalisa ya fice daga APC ya koma jam'iyyar PDP

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya ta ya Tinubu murnan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na dandanlin sada zumunta Tuwita.

Tinubu, ya lashe zaɓen fidda ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC bayan shafe kwanaki ana gudanar da babban taron APC na musamman a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel