Cikakken Tarihin Siyasar Bola Tinubu, 'dan Takarar Shugabancin kasa na jam'iyyar APC

Cikakken Tarihin Siyasar Bola Tinubu, 'dan Takarar Shugabancin kasa na jam'iyyar APC

  • Gogaggen 'dan siyasa, Ahmed Bola Tinubu, ya fara siyasa tun 1992 lokcin da ya shiga jam'iyyar SDP kuma mamba a tsagin People's Front karkashin Musa Yar'adua
  • Ya yi sanata kuma ya shugabanci jihar Legas na tsawon shekaru 8 inda ya kawo cigaba a fannin ilimi, ababen more rayuwa da suka hada da tituna sabbi kuma na zamani
  • Tinubu yana daga cikin jiga-jigan 'yan siyasar Najeriya da suka kafa jam'iyyar maja wacce ta kawo shugaba Buhari kan kujerarsa a 2015 kuma ya zarce a 2019

Bola Ahmed Tinubu, 'dan takarar shugabancin kasa a zaben 2023 a karkashn jam'iyyar APC, ya dade yana jan zarensa a siyasar Najeriya.

Tarihin siyasar fitaccen 'dan siyasan za a iya danganta shi tun daga shekarar 1992 lokacin da ya shiga jam'iyyar SDP inda ya zama mamban tsagin People's Front karkashin jagorancin marigayi Shehu Musa Yar'adua tare da sauran 'yan siyasa kamar su Umaru Yar'adua, Atiku Abubakar, Babagana Kingibe, Rabiu Kwankwaso, Abdullahi Aliyu Sumaila, Magaji Abdullahi, Dapo Sarumi da Yomi Edu.

Kara karanta wannan

Kayi watsi da maganar addini ko kabila wajen zaben mataimakinka: Mataimakan gwamnoni ga Tinubu

Cikakken Tarihin Siyasar Bola Tinubu, 'dan Takarar Shugabancin kasa na jam'iyyar APC
Cikakken Tarihin Siyasar Bola Tinubu, 'dan Takarar Shugabancin kasa na jam'iyyar APC. Hoto daga channelstv.com
Asali: Depositphotos

An zabe shi matsayin sanata da ya wakilci mazabar Legas ta yamma a jamhuriya ta uku wacce ba ta dade ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan fitar sakamakon zaben 1993 da aka soke, Tinubu zama mamban wata kungiya mai suna National Democratic Coalition wacce ta ke fafutukar dawo da damokaradiyya tare da tabbatar da Moshood Abiola a matsayin wanda ya ci zaben.

Tinubu ya bar kasar bayan hawa mulkin Janar Sani Abacha a 1994 kuma ya dawo a 1998 bayan mutuwarsa wanda hakan ya kawo shigowar jamhuriya ta hudu.

A zaben 1999, Bola Ahmd Tinubu ya ci zaben kujerar gwamnan jihar Legas a karkashin jam'iyyar Alliance for Democracy.

A shekaru takwas da ya yi yana mulkar jihar Legas, ya taka rawar gani a fannin ilimi, ya daidaita yawan makarantun jihar.

Ya samar da sabbin tituna wadanda suka kasance gata ga jihar sakamakon yadda kullum ta ke kara cika.

Kara karanta wannan

An yi zalunci: Tawagar Yahaya Bello ta caccaki shugabannin APC bisa zaban Tinubu

A 2009, bayan nasarar da PDP ta samu a zaben shugabancin kasa na 2007, Tinubu ya zama na kan gaba wurin kafa jam'iyyar maja wacce ta kalubalanci mulkin PDP.

A 2013, an tattaro jam'iyyun Action Congress of Nigeria (ACN), the Congress for Progressive Change (CPC), the All Nigeria Peoples Party (ANPP), tsagin All Progressives Grand Alliance (APGA) da sabuwar PDP (nPDP) wani tsagi na PDP inda aka kafa APC.

A 2014, Tinubu ya goyi bayan Muhammadu Buhari, wanda shi ne shugaban CPC kuma ya fadi zabukan 20023, 2007 da 2011 da ya nemi kujerar shugaban kasa a APC.

Da farko Tinubu ya so zama mataimakin shugaban kasa amma daga bisani sai ya gabatar da Yemi Osinbajo, makusancinsa kuma tsohon kwamishinan shari'a.

A 2015, Buhari ya ci nasara zaben da aka yi kuma ya kara samun nasara a 2019 inda ya lallasa Jonathan a karon farko ya kuma make Atiku a karo na biyu.

Kara karanta wannan

Kiristoci yan arewa 4 da dayansu zai iya zama abokin takarar Tinubu

Tinubu ya samu nasarar zama 'dan takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar APC inda zai kara da Atiku Abubakar daga jam'iyyar PDP tare da sauran 'yan siyasa masu neman kujerar shugabancin kasa a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng