Kiristoci yan arewa 4 da dayansu zai iya zama abokin takarar Tinubu

Kiristoci yan arewa 4 da dayansu zai iya zama abokin takarar Tinubu

  • Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya lashe tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC)
  • Tsohon gwamnan na jihar Lagas ya samu kuri’u 1,271 bayan an gama tattara sakamakon zaben a ranar Laraba, 8 ga watan Yuni
  • Tinubu zai fafata a zaben shugaban kasa na 2023 tare da dan takarar PDP, Atiku Abubakar da sauran yan takara

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Komai ya kammala a bangaren Asiwaju Bola Ahmed Tinubu domin ya zabi abokin takararsa na zaben shugaban kasa na 2023 bayan ya yi nasarar zama wanda zai daga tutar jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

A bisa ga jadawalin da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta saki, ana sa ran yan takarar shugaban kasa za su zabi abokan takararsu kafin karfe 12:00 na tsakar dare a ranar Alhamis, 9 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: A shirye nake na yiwa Tinubu aiki kamar yadda na yiwa Lawan – Orji Kalu

Kiristoci yan arewa 4 da dayansu zai iya zama abokin takarar Tinubu
Kiristoci yan arewa 4 da dayansu zai iya zama abokin takarar Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Tinubu
Asali: Facebook

Ana ta rade-radi a cikin APC cewa Tinubu zai dauki dan arewa kirista, musamman ma da yake yan Najeriya na adawa da tikitin Musulmi-Musulmi.

Idan Tinubu ya yanke shawarar daukar dan arewa kirista, akwai jerin sunayen mutane hudu da za a iya zaban daya a cikinsu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sun hada da:

1. Hon Yakubu Dogara

Dogara wanda yake haifaffen dan jihar Bauchi ya kasance tsohon kakakin majalisar wakilai. Ana kallonsa a matsayin dan siyasa mai karfi a arewacin Najeriya, musamman yadda ‘yan majalisar arewa suka mara masa baya a 2015 duk da cewar shugabannin jam’iyyar sun so Femi Gbajabiamila ne a wancan lokacin.

Dogara mai shekaru 54 ya dace da tsarin fitaccen dan siyasa, wanda ke da tasiri a siyasance kuma abokin takara mai jini a jika da zai jera da tsoho kamar Tinubu.

Kara karanta wannan

Ekiti 2022: Jerin sunayen yan takara 16 da za su fafata a zaben gwamna

2. Boss Mustapha

Mutane da dama sun ce za a iya zabar shi saboda alakarsa da Tinubu a zamanin da suke jam’iyyar Social Development Party a 1992.

Mustapha mai shekaru 66 shine babban sakataren gwamnatin tarayya a yanzu haka. Ya kasance lauya daga jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Ana ganin mutuncinsa sosai a jam’iyyar APC kuma yana da tasiri sosai a tsakanin masu rike da madafun iko a jam’iyyar.

3. Simon Lalong

Wata kila shine ya fi kowa gogewa a cikin wadanda za a iya tsayarwa a matsayin abokan takara saboda ya dandani mulki daga bangaren zartarwa da na dokoki.

A yanzu haka Lalong mai shekar 59 shine gwamnan jihar Plateau kuma ya kasance tsohon kakakin majalisar dokokin jihar. Kuma a yanzu ma shine shugaban kungiyar gwamnonin arewa.

Sai dai akwai shakku game da shahararsa a arewa, amma takwarorinsa na iya marawa takararsa baya, musamman a yanzu da suka zama masu karfi da fada aji a cikin jam’iyyar mai mulki.

Kara karanta wannan

Kusoshi a Jam’iyya sun dage Tinubu ya dauki Mataimaki daga mutum 2 a Gwamnatin Buhari

4. Babachir Lawal

Lawal ya kasance tsohon sakataren gwamnatin tarayya. Dan siyasar mai shekaru 67 kuma haifaffen jihar Adamawa ya kasance dan kashenin Tinubu kuma ya na hannun damansa tsawon shekaru da dama.

Alakarsa da Tinubu na iya bashi damar darewa wannan matsayin, amma rashin shahararsa da shari’arsa ta rashawa da ke kotu a yanzu haka na iya kawo masa cikas.

Lagit.ng Hausa nemi jin ra’ayin wani mai bibiyar lamuran siyasar kasar mai suna Mallam Muhammad Auwal kan batun tsayar da Kiristan arewa inda ya ce:

“Tabbas Musulman Arewa sun ninninka kiristocin Arewa yawa, amma duba da halin rashin yarda da juna da ake ciki a yankin sakamakon rikice rikicen addini da na ƙabilanci daya dabaibaye Arewa, abu ne mai kamar wuya Tinubu ya samu goyon bayan Musulman Arewa idan har ya ɗauki Kiristan Arewa a matsayin mataimakinsa.
“Shi ma Tinubu wannan ne kaɗai dalilin da yasa ba zai kuskura ɗaukan Kiristan Arewa ba. Ta yaya ake tunanin Kiristan Arewa zai kawo ma Tinubu ƙuri'un Kano, Katsina, Borno, Kaduna da Jigawa?

Kara karanta wannan

Abokin takara: Atiku na daf da daukar Gwamna mai-ci, Tinubu zai tafi da tsohon Gwamna

“Haka zalika gwamnonin jam'iyyar APC daga yankin Arewa su 14 sun taka rawar gani wajen samun nasarar Tinubu a zaɓen fidda gwani, kuma a irin siyasarmu ta 'ba ni gishiri in baka manda' su ɗinne kuma zasu yi ruwa su yi tsaki wajen taya shi zaɓar mataimaki musamman daga yankin nasu."

Jerin mutane 6 da suka marawa Yemi Osinbajo baya akan Bola Tinubu

A gefe guda, mun ji cewa tsohon gwamnan jihar Lagas, Bola Ahmed Tinubu ya lallasa duk sauran yan takara, musamman tsohon dansa a fannin siyasa, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, wajen zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

An gudanar da zaben fidda dan takarar ne a filin Eagle Square da ke babbar birnin tarayya Abuja.

Ku tuna cewa a 2017, Yemi Osinbajo ya ce bai taba haduwa da Bola Tinubu ba lokacin da ya nada shi a matsayin Atoni Janar kuma kwamishinan shari’a a jihar Lagas a lokacin mulkinsa.

Kara karanta wannan

Takarar Musulmi da musulmi: Ana yiwa Tinubu zagon kasa ne, in ji wani fasto

Asali: Legit.ng

Online view pixel