An yi zalunci: Tawagar Yahaya Bello ta caccaki shugabannin APC bisa zaban Tinubu

An yi zalunci: Tawagar Yahaya Bello ta caccaki shugabannin APC bisa zaban Tinubu

  • Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello ya yi watsi da fitowar Bola Tinubu a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC
  • Gwamna Bello ya ce tsarin da ya kawo aka ba da tikitin takarar ga Tinubu ba daidai ba ne kuma an jirkita shi
  • Gwamnan mai shekaru 47 ya kuma yi zargin cewa akwai wasu jiga-jigan ‘yan masu fada a ji da gwamnonin APC na Arewa da ke shirya masa makarkashiya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja – Kungiyar yakin neman zaben Yahaya Bello na neman shugaban kasa ta caccaki fitowar Bola Tinubu a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Punch ta ruwaito.

Sun bayyana hakan ne a wata sanarwa da suka fitar a ranar Laraba, 8 ga watan Yuni mai taken, ‘Yahaya Bello ne dai gwarzon wadanda aka zalunta.'

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Malik Ado-Ibrahim ya lashe tikitin takarar a YPP ta su Adamu Garba

An yi magudi, bai kamata Tinubu ya lashe zabe ba, inji Yahaya Bello
Akwai magudi: Tawagar Yahaya Bello ta caccaki 'yan APC bisa zaban Tinubu | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

A cikin sanarwar da mai magana da yawun kungiyar, Yemi Kolapo, ya fitar kuma Legit.ng ta gani, ya bayyana atisayen zaben fidda gwnain APC a matsayin wani tsari da aka samu matsala a cikinsa.

Wani bangare na sanarwar ya bayyana cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Zaben fidda gwani na jam'iyyar All Progressives Congress ya zo kuma ya wuce. Tsarin ya kasance cikin kwanciyar hankali amma an dagula shi.
“Duk da haka wannan ba sabon abu bane a kasar da aka ayyana dimokuradiyya a matsayin gwamnatin azzalumai daga saboda azzalumai."

Wannan martani na tawagar Yahaya Bello na zuwa ne jim kadan bayan da aka ayyana Bola Ahmed Tinubu a matsayin dan takarar da ya lashe zaben shugaban kasa a jam'iyyar APC

Kafin nan, Yahaya Bello dama ya nuna bacin ransa da yadda gwamnonin APC ke ta bayyana zawarcin tikitin jam'iyyar ga yankin Kudancin Najeriya.

Kara karanta wannan

An yi abin kunya: Bidiyon yadda Yahaya Bello ya kauracewa shugaban APC na kasa

Tuni dai Bello ya bayyana cewa, akwai wasu jiga-jigan APC da ke shirya masa makarkashiya don rasa damar yin takara a jam'iyyar ta APC.

An yi abin kunya: Bidiyon yadda Yahaya Bello ya kauracewa shugaban APC na kasa

A bangare guda, jaridar PM News ta nuna wani bidiyo na Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi inda ya nuna kamar rashin mutuntawa ga shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu a zaben fidda gwani na shugaban kasa a jam'iyyar da ke gudana a dandalin Eagle Square dake Abuja.

Bello, wanda ya zo karramawa da gaisawa da shugabannin APC da gangan ya ki ya gaisa da Adamu, wanda shi ne kan-kat a shugabannin APC.

Dan takarar shugaban kasan na jam’iyyar APC ya yi musabaha da tsaffin shugabannin jam’iyyar APC, John Odigie-Oyegun, Cif Bisi Akande da Adams Oshiomhole sannan ya wuce Adamu inda suka gaisa da Aisha Buhari da kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Kebbi: Shugaban masu rinjaye a majalisa ya fice daga APC ya koma jam'iyyar PDP

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel