Kayi watsi da maganar addini ko kabila wajen zaben mataimakinka: Mataimakan gwamnoni ga Tinubu

Kayi watsi da maganar addini ko kabila wajen zaben mataimakinka: Mataimakan gwamnoni ga Tinubu

  • Mataimakan gwamnonin Najeriya masu murabus sunce kada Tinubu ya damu da lamarin addini wajen zaben mataimaki
  • Ana mujadala kan shin zai kyautatu Tinubu ya zabi Musulmi ya zama mataimakinsa duk da shima Musulmi ne
  • Asiwaju Bola Tinubu ya lashe zaben fidda gwanin dan takaran shugaban kasa karkashin jam'iyyar APC

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Kungiyar tsaffin mataimakan gwamnonin Najeriya karkashin jam'iyyar All Progressives Congress APC sun shawarci uwar jam'iyya tayi watsi da maganar addini da kabila wajen zaben mataimakin Tinubu.

Kungiyar ta bayyana hakan ne ranar Alhamis a hira da manema labarai a birnin tarayya Abuja, rahoton Punch.

Shugaban kungiyar kuma tsohon mataimakin gwamnan jihar Edo, Lucky Imasuen, tare da takwarorinsa suka halarci hirar.

Sun hada da tsohon mataimakin gwamnan Bauchi, Abdulmalik Mahmood; Armaya’u Abubakar na Taraba, Nkem Okeke na Anambra, Ahmed Ibeto na Neja, Abdullahi Gwarzo na Kano, Bello Tukur na Adamawa da Femi Pedro na Legas.

Kara karanta wannan

Neman Mataimkin Atiku: PDP Ta Kafa Kwamiti A Yayin Da Wike Da Okowa Ke Neman Zama Mataimakin Shugaban Kasa

Tinubu
Kayi watsi da maganar addini ko kabila wajen zaben mataimakinka: Mataimakan gwamnoni ga Tinubu Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Imasuen yace:

"Kungiyar na kira da dan takaran shugaban kasarmu, Tinubu, da masu ruwa da tsakin jam'iyyarmu su duba hakkin demokradiyya wajen zaben mataimaki."
"Mun yi imani Tinubu zai iya gudanar da lamuran Najeriya ba tare da damuwa da lamarin addini ko kabila ba."

Imasuen yace kungiyarsu na da mambobi 50 daga APC kuma 62 daga sauran jam'iyyu.

Asiwaju Bola Tinubu ya lashe zaben fidda gwanin jam'iyyar APC

Tsohon gwamna jihar Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya lashe zaben fidda gwanin yan takaran shugaban kasa karkashin jam'iyyar All Progressives Congress APC.

A zabensa na farko tun bayan barin mulki a 2007, Tinubu yanzu shine zai wakilci jam'iyyar PDP a zaben shugaban kasa a zaben shekarar 2023.

Tinubu ya lallasa yan takara 12 da suka fafata a zaben inda ya samu kuri'u sama da 1,271

Kara karanta wannan

Tinubu ya mamayi Farfesa Osinbajo, ya kai masa ziyara kwatsam har ofishinsa a Aso Villa

Wanda ya zo na biyu shine tsohon Gwamnan jihar Rivers, kuma tsohon Ministan Sufuri Rotimi Amaechi wanda ya samu kuri'u 316.

Sannan Farfesa Yemi Osinbajo wanda ya samu kuri'u 235.

Asali: Legit.ng

Online view pixel