‘Dan takaran PDP a 2015 da 2019, tsofaffin kusoshin APC za su yi wa NNPP takarar Gwamna
- Malam Aminu Ringim shi ne wanda jam’iyya mai kayan marmari ta ba takarar Gwamna a Jigawa
- Injiniya Nura Khalil da John James Akpanudoedehe za su rikewa NNPP tuta a Akwa Ibom da Katsina
- Wadanda za su yi wa jam’iyyar hamayyar takarar Gwamnoni a jihohi sun taba yin PDP ko kuma APC
Nigeria - Aminu Ringim wanda ya taba neman takarar gwamna a karkashin jam’iyyar PDP shi ne zai yi wa NNPP takara a jihar Jigawa a zabe mai zuwa.
Rahoton da hukumar dillancin labarai na kasa ta fitar ya bayyana cewa Aminu Ringim ya samu takara babu hamayya ne a karkashin jam’iyyar ta NNPP.
Musa Abubakar wanda NNPP ta tura a matsayin malamin zabe ya tabbatar da nasarar Ringim bayan an nemi jin ta bakin masu kada zaben tsaida gwani.
A cewar Musa Abubakar, masu zabe 861 aka tantance daga kananan hukumomi 27 na Jigawa, kuma sun tabbatar da Ringim a matsayin wanda aka ba tikiti.
Ringim bai da hamayya a NNPP
Kamar yadda rahoto ya bayyana, babu wanda ya yi takara tare da Ringim a NNPP. Da yake jawabi, ya godewa ‘yan jam’iyya da suka tabbatar da takarar ta shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
‘Dan takarar ya ce an kawo NNPP ne domin ta canji jam’iyyun da ke mulki, yake cewa jam’iyyar ta na karkashin jagorancin irinsu Dr Rabiu Musa Kwankwaso.
Ringim wanda aka fi sani da Malam, shi ne ya yi wa PDP takara a Jigawa a zabukan 2015 da 2019.
Khalil ya doke Ibrahim Zakari
A jihar Katsina kuwa, labarin da mu ka samu shi ne, Injiniya Nura Khalil ne aka tabbatar a matsayin ‘dan takarar gwamna a jam’iyya mai kayan dadi.
Nura Khalil wanda ya samu kuri'u 950 ya nemi kujerar gwamna a jihar Katsina a karkashin jam’iyyar ANPP. Ibrahin Zakari ya zo na biyu da kuri'u 29.
NNPP ta shiga zabe a Akwa Ibom
The Cable ta fitar da rahoto cewa tsohon sakataren APC na kasa, John Akpanudoedehe ya samu takarar kujerar gwamnan Akwa Ibom a jam’iyyar adawar.
Shi ma John Akpanudoedehe ya samu takarar ne ba tare da hamayya a NNPP ba. A shekara mai zuwa zai gwabza da ‘yan takaran APC da na PDP a Akwa Ibom.
Hunkuyi zai yi takara a Kaduna
Ku na da labari Sanata Suleiman Othman Hunkuyi ya tabbata 'dan takarar gwamna na jam'iyyar NNPP mai kayan marmari a zaben 2023 a Jihar Kaduna.
Tsohon Sanatan na Arewacin jihar Kaduna ya yi nasarar zama dan takarar na NNPP ne bayan ya samu kuri'u 730 yayin da aka tsaida Abba K. Yusuf a Kano.
Asali: Legit.ng