Ndume Ya Goyi Bayan Buhari: Babu Shugaban Ƙasa Da Ba Zai Zaɓi Magajinsa Ba

Ndume Ya Goyi Bayan Buhari: Babu Shugaban Ƙasa Da Ba Zai Zaɓi Magajinsa Ba

  • Sanata Ali Ndume, Tsohon shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa ya goyi bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya zabi wanda ya ke son ya gaje shi
  • Shugaban kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na Rotimi Amaechin ya ce hakan bai saba wa demokradiyya ba inda ya bada misalin cewa a Amurka ma Barrack Obama ya zabi Joe Biden
  • Ndume ya kuma ce gwamnonin Najeriya ma sun zabi wadanda suke son su gaje su don haka shima Shugaba Muhammad Buhari ya kamata a bashi wannan damar

Tsohon shugaban marasa rinjaye a majalisa kuma shugaban kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na Rotimi Amaechi, Sanata Ali Ndume, APC, Borno South ya goyi bayan kalaman Buhari game da magajinsa yana mai cewa hakan bai saba wa demokradiyya ba.

Kara karanta wannan

Jerin sunayen 'yan takara 5 da ake sa ran Buhari zai zabi daya don ya gaje shi

A hirar da Vanguard ta yi da shi, Sanata Ndume ya ce babu wani matsala idan Buhari yana son ya zabi magajinsa, yana mai cewa babu wani shugaba da ba zai zabi magajinsa ba ko ya so sanin wanda zai maye gurbinsa.

Ndume Ya Goyi Bayan Buhari: Babu Shugaban Ƙasa Da Ba Zai Zaɓi Magajinsa Ba
Ndume Ya Goyi Bayan Buhari: Babu Shugaban Ƙasa Da Ba Zai Zaɓi Magajinsa Ba. Hoto: Vanguard.
Asali: Twitter

Ko a Amurka shugabanni suna zaben magadansu, Ndume

Ndume ya ce tsohon shugaban Amurka, Barrack Obama ya zabi Joe Biden ya gaje shi kuma ya yi aiki tukuru domin tallafawa Biden, yana mai cewa babu wani matsala tare da kalamen na Shugaba Buhari.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Babu wani matsala tare da bukatar Shugaba Buhari na neman zaben wanda ya ke son ya gaje shi, ya dace da demokradiyya. Babu wani Shugaba da ba zai bayyana wanda ya ke son ya gaje shi ba.
"Da takaici ya kama ni idan Shugaban Kasar bai ambaci wanda ya ke son ya gaje shin ba. Kamar yadda ya ce, an kyalle Gwamnoni sun zabi magadansu, a bar shugaban kasar shima ya zaba. Babu wani matsala idan shugaban kasar ya yi haka."

Kara karanta wannan

2023: 'Yan Kudu Surutu Kawai Suka Iya, Arewa Za Ta Fitar Da Shugaban Ƙasa, In Ji Babban Fasto a Najeriya

Buratai: Tsohon Babban Hafsan Sojojin Ƙasan Najeriya Ya Ba Wa APC Gudunmawar Motar Kamfen Ƙirar Najeriya

A wani rahoton, tsohon babban hafsan sojin kasa kuma Jakadan Najeriya a Jamhuriyar Benin, Janar Tukur Buratai; Babban Kwamishinan Najeriya a Jamhuriyar Zambia, Nwanebike Oghi da kuma wasu jakadu na musamman a ranar Laraba sun bai wa shugabancin jam’iyyar APC kyautar motoci kirar bas mai daukar mutum 18.

Farar motar, wacce kamfanin Innoson Motors ne ya kerata sabuwa ce kuma a jikinta a rubuta “Jakadu na musamman ne su ka bayar da kyautarta,” The Punch ta ruwaito.

Sun gabatar da motar ne a babban ofishin jam’iyyar da ke Abuja bayan wakilan sun yi taron sirri da shugaban jam’iyyar, Sanata Abdullahi Adamu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel