Jerin sunayen 'yan takara 5 da ake sa ran Buhari zai zabi daya don ya gaje shi

Jerin sunayen 'yan takara 5 da ake sa ran Buhari zai zabi daya don ya gaje shi

A ranar Talata, 31 ga watan Mayu ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wani jawabi wanda ke ci gaba da haddasa cece-kuce, ya ce zai so ya zabi wanda yake so ya gaje shi gabannin zaben 2023.

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Har zuwa lokacin da ya yi jawabin na ranar Talata, yan takarar kujerar shugaban kasar na APC wadanda suka fi 20 suna ta zuba idanu don zuwan ranar zaben fidda gwani wanda aka shirya yi a ranar 6 ga watan Yuni.

Sai dai kuma, tsarin ya sauya a yanzu domin shugaba Buhari ya bukaci gwamnonin APC su taimaka masa da aikin zabar wanda suke ganin ya kamata ya gaje shi.

Jerin sunayen 'yan takara 5 da ake sa ran Buhari zai zabi daya don ya gaje shi
Jerin sunayen 'yan takara 5 da ake sa ran Buhari zai zabi daya don ya gaje shi Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Abun da hakan yake nufi a takaice shine cewa shugaban kasar yana duba yiwuwar zabar wanda zai daga tutar jam’iyyar ta hanyar maslaha maimakon yin takara.

Kara karanta wannan

Rudani: Sabbin bayanai sun fito, yayin da gwamnonin APC ke shawari kan zaban magajin Buhari

Tun bayan umurnin nasa na ranar Talata, gwamnonin na ta zama domin fitar da wanda za su iya zaba a matsayin wanda suka fi so a tsakanin yan takara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayin da gwamnonin APC ke ci gaba da neman magajin Buhari, wannan zauren ya yi hasashen yan takarar shugaban kasa biyar da za su iya cin moriyar wannan sabon tsarin.

1. Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan

An sanar da Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, wasu jiga-jigan APC biyu, Orji Uzor Kalu da Femi Fani-Kayode, sun fitar da wasu jawabai inda suka shawarci shugaba Buhari da shugabannin jam’iyyar a kan suma su fitar da dan takara daga arewa.

Musamman Sanata Kalu ya bukaci cewa a mika tikitin ga arewa maso gabas yankin da Atiku ya fito domin rage farin jininsa.

Kara karanta wannan

2023: Buhari ya lissafa sharuddan da dole 'dan takarar shugabancin kasa na APC ya cika

Idan har APC ta bi wannan shawarar, shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ne kan gaba a yan takarar yankin da za a iya dauka.

2. Yemi Osinbajo

Idan har APC ta yanke shawarar mika mulki ga kudu, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo na daya daga cikin manyan yan takarar yankin da za a iya dauka.

Yana da farin jinin siyasa a fadin kasar kuma yana daya daga cikin yan tsirarun yan takara da basu da guntun kashi a tsuliyarsu.

3. Asiwaju Bola Ahmed

Masana sun sha fadin cewa idan har APC ta yanke shawarar mika tikitinta ga yankin kudu, toh Asiwaju Bola Tinubu ne dan takarar da zai iya yin gaba da gaba da Atiku ko kuma kowani dan takara daga Arewa.

Tsawon shekaru masu yawa, ya gina kyakkyawar alaka ta siyasa daga kudu zuwa arewa. Ana kuma ganin shi kadai ne dan takarar shugaban kasa na APC da ke da kudin fafatawa da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku.

Kara karanta wannan

2023: Duk da nukun-nukun da ake yi, akwai yiwuwar APC ta tantance Jonathan a yau

4. Rotimi Amaechi

Baya ga Tinubu, wani dan takarar shugaban kasa daga kudu wanda ke da farin jini a kasar shine tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi.

Rawar ganin da Amaechi ya taka a shugabancin Buhari cikin shekaru bakwai da suka shige ya sa siyasarsa ta kara karfi wanda ba za a iya watsi da shi ba.

5. David Umahi

A farkon taron da gwamnonin APC wadanda za su zabi magajin Buhari suka gudanar, majiyoyin sun ce wasu sun nemi a zabi gwamnoni biyu (daya daga kudu sannan daya daga arewa).

Idan har wannan shawara ta samu karbuwa, ana iya zabar Gwamna Umahi a matsayin magajin Buhari koda dai damar da yake da ita na mallakar tikitin bata da karfi.

Gaskiyar magana: Jigo ya yi karin-kashe a kan sauya-shekar Tinubu daga APC zuwa SDP

A wani labarin, a ranar Laraba, 1 ga watan Yuni, 2022, aka rahoto tsohon gwamnan jihar Ekiti, Segun Oni yana ma magana game da sauya-shekar Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Buhari ya shiga ganawa da gwamnonin APC kan zaben magajinsa

Segun Oni ya nuna cewa babu abin da ke nuna tabbas Bola Tinubu zai shiga jam’iyyar hamayyarsu Social Democratic Party da aka fi sani da SDP.

Rahoton da Daily Trust ta fitar ya ce Oni ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa wasu tambayoyin da menama labarai suka yi masa jiya a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel