Ni masoyin Arewa ne, zan lallasa Atiku a 2023, 'yan Adamawa ni za su zaba, inji Okorocha

Ni masoyin Arewa ne, zan lallasa Atiku a 2023, 'yan Adamawa ni za su zaba, inji Okorocha

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Rochas Okorocha ya bayyana yankin da aka fi sonsa da kuma girmama shi a Najeriya
  • Tsohon gwamnan na jihar Imo ya ce duk 'yan takara ya yi fice saboda ana son sa a Arewa fiye da ko ina, hakan kuma na iya ba shi damar samun nasara a zaben 2023
  • Okorocha ya lura cewa yana da karfin kayar da dan takarar PDP, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, har ma a jiharsa ta Adamawa a zabe mai zuwa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Imo kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Rochas Okorocha, ya ce burinsa na siyasa ya fi kasuwa a Arewacin Najeriya fiye da kowane yankunan kasar nan, inji rahoton Daily Trust.

Okorocha ya bayyana haka ne a lokacin da yake magana kan batutuwan da suka shafi zaben fidda gwani na jam’iyyar APC mai mulki.

Kara karanta wannan

EFCC ta saki Rochas Okorocha, an tantance shi a matsayin ‘Dan takara kafin a rufe kofa

Ni masoyin Arewa ne, zan lallasa Atiku a 2023, 'yan Adamawa ni za su zaba, inji dan takarar APC Okorocha
Ni masoyin Arewa ne, zan lallasa Atiku a 2023, 'yan Adamawa ni za su zaba, inji Okorocha | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Okorocha dai na fuskantar tuhume-tuhume 17 bisa zargin karkatar da kudade daga asusun hadin gwiwa na gidan gwamnatin Imo da na kananan hukumomi zuwa wasu kamfanoni masu zaman kansu tsakanin shekarar 2014 zuwa 2016.

Bisa kamun da ya sha, kadan ya hana ya rasa damar tantancewar shugabannin APC na 'yan takarar shugaban kasa da aka gudanar, rahoton Independent.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tantance Okorocha ranar Talata

Bayan da wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belin Okorocha a ranar Talata, 31 ga watan Mayu, ya nufi wurin da aka gudanar da aikin tantance 'yan takarar shugaban kasa na APC.

Game da cancantar sa na tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Okorocha ya ce:

“Abin tambaya a yanzu shi ne: wane ne mutumin da zai iya lashe kuri’u kamar NA Buhari don ya kayar da wannan mutumin? Abin da ya kamata ya shagala a tunanin APC kenan.

Kara karanta wannan

2023: Buhari ya lissafa sharuddan da dole 'dan takarar shugabancin kasa na APC ya cika

“Kuma duk wani abu da ya tafi da wata fahimta, to, gazawa ce a wajenmu, kuma abin da ya kamata mu sani kenan, wane dan Najeriya ne zai iya samu kuri’u daga Arewa domin kawai abin da PDP ke alfahari da ita a yanzu shi ne su jawo kuri'un daga Arewa, gaskiya ne hakan.
“Kuma ba lallai Shugaba Buhari ya sake tsayawa zabe ba saboda yawancin mutanen da suka ci tikitin APC a Arewa sun samu ne saboda Shugaba Muhammadu Buhari.
"Kuma a matsayinsa na shugaban kasa da ya yi shekara takwas da kalubalen da ya fuskanta, watakila ba zai iya kawo wadannan kuri’u ba, kuma ba zai sake tsayawa zabe ba, don haka kuna da kalubale. Don haka sai a nemi wanene wancan mutumin da Arewa za ta iya duba ta ba shi kuri’a?
“Kuma ina ganin ni ne wannan domin na fi karbuwa a Arewa fiye da ko’ina. Ni masoyin Arewa ne.”

Kara karanta wannan

Takarar 2023: Shehu Sani ya shawarci Atiku kan irin wanda ya kamata ya zaba a matsayin mataimaki

Okorocha, wanda shi ne Sanata mai wakiltar Imo ta Yamma, jami’an EFCC sun kama shi a gidansa da ke Abuja a ranar 25 ga watan Mayu.

Dan takarar APC: Abu mai sauki ne na lallasa Atiku a zaben 2023, a bani tikiti kawai

A wnai labarin, wani rahoton Punch ya ce, Fasto Tunde Bakare, ya bayyana kwarin gwiwar ganin ya kayar da dan takarar shugaban kasa na PDP, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, idan har aka ba shi tikitin jam’iyyar APC.

Yayin da yake jawabi ga manema labarai, dan takarar shugaban kasar ya bayyana gamsuwa da tsarin tantancewar da APC ta gudanar.

Ya bayyana dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya cancanta a a matsayin abokin gwabzawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel