Dan takarar APC: Abu mai sauki ne na lallasa Atiku a zaben 2023, a bani tikiti kawai

Dan takarar APC: Abu mai sauki ne na lallasa Atiku a zaben 2023, a bani tikiti kawai

  • Daya daga cikin 'yan takarar APC ya bayyana manufarsa ta cin zabe, inda yace yana da tabbacin kayar da Atiku
  • Ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai kan lamurran da suka shafi zabe
  • Ya kuma bayyana wasu abubuwan da aka tambayi 'yan takarar da jam'iyyar APC ta tantance a kwanakin nan

Abuja - Wani rahoton Punch ya ce, Fasto Tunde Bakare, ya bayyana kwarin gwiwar ganin ya kayar da dan takarar shugaban kasa na PDP, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, idan har aka ba shi tikitin jam’iyyar APC.

Yayin da yake jawabi ga manema labarai, dan takarar shugaban kasar ya bayyana gamsuwa da tsarin tantancewar da APC ta gudanar.

Ya bayyana dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya cancanta a a matsayin abokin gwabzawa.

Kara karanta wannan

Bidiyon Atiku da iyalansa suna kwasar rawa bayan nasararsa a zaben fidda gwanin PDP

Zan lallasa Atiku a zabe mai zuwa, Tunde Bakare
Dan takarar APC Bakare: Abu mai sauki ne na ragargaza Atiku a zaben 2023 | Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa, da aka tambaye shi game da tantance 'yan takara ta APC, sai ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Aikin tantancewar ya yi kyau sosai. An yi tambayoyi da suka dace game da yadda za mu gyara matsalolin da ke addabar al'ummarmu kuma an ba su amsoshin da suka dace.
“Da yardar Allah, mun yi farin ciki da cewa muna da abin da za mu bayar ga wannan al’umma. A cikin wannan mawuyacin lokaci a tarihinmu, babu wanda zai iya cewa yana da dukkan mafita."

Hakazalika, ya ce ya shaidawa kwamitin tantancewar APC zai yi iya kokarinsa wajen ganin an samu shugabanci nagari daga bangarensa.

A bangare guda, kamar yadda jam’iyyar adawa ta PDP, APC ma ta yi fatali da bukatar da hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta yi na gudanar da gwaje-gwajen kwayoyi kan 'yan takara.

Kara karanta wannan

Tinubu: Babu wani cin girma da zan yi, burina kawai na yi takara a zaben 2023 mai zuwa

'Yan takarar sun shaida wa manema labarai cewa babu batun gwajin shan kwaya da jam’iyyar ta yi.

An tattaro cewa kwamitin da Cif John Odigie-Oyegun ke jagoranta zai mika rahotonsa ga shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, wanda shi kuma zai mika shi ga shugaban kasa Muhammadu Buhari domin ya dauki matakin karshe.

Shugaban majalisa ya tura wa deliget wasika kan zaben fidda gwanin APC

A wani labarin, Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya aika wasika mai zafi ga deliget-deliget na jam’iyyar APC da su yi la’akari da tarihin ‘yan takara da kuma bayanai kafin kada kuri’a a zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar da ke tafe.

A wata wasika a ranar Laraba, dan takarar shugaban kasar ya nemi kuri’un deliget-deliget domin ya samu damar zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben shugaban kasa na 2023, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shirin zaben fidda gwani: Tinubu, wasu 11 sun tsallake tantancewar shugabannin APC

Ya kuma bukace su da su zabi mutumin da zai yi shugabanci ba mulkin ’yan Najeriya ba da kuma “shugaban da ba shi da kaya kwata-kwata a kansa”.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.