Kwankwaso ya Sanar da Babban Mukamin da Za a Bai wa Peter Obi da Ya Koma NNPP

Kwankwaso ya Sanar da Babban Mukamin da Za a Bai wa Peter Obi da Ya Koma NNPP

  • Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso na jihar Kano, ya ce da Peter Obi ya koma NNPP, da shi ne zai kasance masa abokin takara
  • Kwankwaso, wanda suka gana da Obi kwanaki kadan kafin ya koma Labour Party, ya ce matsalolin kasa kadai suka tattauna
  • Tsohon gwamnan jihar Kanon, wanda shi ne dan takarar shugabancin kasa a jam'iyyar NNPP ya aike fatan alheri ga dukkan 'yan takarar shugabancin kasa

Rabi'u Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano, ya ce Peter Obi, dan takarar shugabancin kasa a Labour Party, shi ya dace ya zama abokin takarar shi idan da ya koma jam'iyyar NNPP.

Kwankwaso ya yi wannan batun ne a wata tattaunawa da yayi da Channels TV.

Kwankwaso ya Sanar da Babban Mukamin da Za a Bai wa Peter Obi da Ya Koma NNPP
Kwankwaso ya Sanar da Babban Mukamin da Za a Bai wa Peter Obi da Ya Koma NNPP. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

A ranar 27 ga watan Mayun, Obi ya koma Labour Party sa'o'i kadan bayan sanar da fitarsa daga jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Atiku, Obi, NNPP da wasu abubuwa 5 da Kwankwaso ya yi magana a hirar da aka yi da shi

Kafin tsohon gwamnan ya koma LP, akwai hasashe da ke nuna cewa Obi na iya hada kai da Kwankwaso a NNPP domin takarar shugabancin kasa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A ranar Litinin, Obi ya tabbatar dan takarar shugabancin kasa a LP bayan wasu 'yan takara uku sun ja baya.

A daya bangaren, Kwankwaso shi ne dan takara daya tak na shugabancin kasa karkashin jam'iyyar NNPP.

Da aka tambaye shi ko Obi ya tuntube shi kan komawa NNPP, Kwankwaso ya ce sun tattauna kan lamurran kasa tare da tsohon gwamnan Anambra kwanaki kadan kafin ya koma LP.

"Toh, a gaskiya mun samu damar tattaunawa da juna kan lamurran kasa, bayan kwanaki kadan sai ya bayyana a Labour Party wanda yanzu shi ne dan takarar shugabancin kasa," yace.
"Ina masa fatan alheri kuma ina yi wa sauran 'yan takarar shugabancin kasa fatan alheri. Ina da tabbacin jama'ar kasar ne za su yanke hukuncin a yayin zabe a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023."

Kara karanta wannan

Ba zan yi amai na lashe ba: Martanin gwamna Wike da ya sha kaye bayan ganawa da Atiku

Da aka tambaye shi ko zai iya karbar Obi a matsayin mataimaki, tsohon gwamnan Kanon ya ce mutane da yawa sun kawo wannan shawarar.

"Mutane da yawa sun kawo wannan shawara. Na amince hakan zai iya yuwuwa da bai shiga wata jam'iyyar ba. A yanzu, dan takarar wata jam'iyyar ne kamar yadda muka gani a labarai. Muna zuba ido mu ga abinda zai faru nan da makonni kadan," ya kara da cewa.

Allah ne ya aiko Kwankwaso ya fatattaki yunwa, ya hada kan 'yan Najeriya, NNPP

A wani labari na daban, jam'iyyar NNPP ta kwatanta dan takarar shugabancin kasa a karkashin ta, Sanata Rabiu Kwankwaso a matsayin "ma'aikin Ubangiji" wanda yake son yakar yunwa da sake hada kan Najeriya.

Rahoton Daily Nigerian ya ce, Rabaren Emma Agubanze, mamban kwamitin tuntuba na addini na NNPP ya sanar da hakan a Legas a ranar Laraba. Ya ce za a yi zaben 2023 lafiya kalau kuma Kwankwaso ne da jam'iyyar za su yi nasara.

Kara karanta wannan

Ainahin dalilin da yasa Tambuwal ya janyewa Atiku – Kungiyar yakin neman zabensa

Asali: Legit.ng

Online view pixel