Allah ne ya aiko Kwankwaso ya fatattaki yunwa, ya hada kan 'yan Najeriya, NNPP

Allah ne ya aiko Kwankwaso ya fatattaki yunwa, ya hada kan 'yan Najeriya, NNPP

  • Jam'iyyar NNPP ta sanar da cewa Allah ne ya aiko Kwankwaso domin ya fatattaki yunwa kuma ya hada kan 'yan Najeriya baki daya
  • Rabaren Emma Agubanze ya sanar da hakan a Legas inda yace taimakon Ubangiji ya bayyana a Najeriya kuma jam'iyyar NNPP daga Ubangiji ta ke
  • Ya yi kira ga 'yan Najeriya da su garzayo tare da shiga jam'iyyar saboda ko shakka babu Kwankwaso zai ci zabe kuma nasara ta jam'iyyar ce

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Legas - Jam'iyyar NNPP ta kwatanta dan takarar shugabancin kasa a karkashin ta, Sanata Rabiu Kwankwaso a matsayin "ma'aikin Ubangiji" wanda yake son yakar yunwa da sake hada kan Najeriya.

Rahoton Daily Nigerian ya ce, Rabaren Emma Agubanze, mamban kwamitin tuntuba na addini na NNPP ya sanar da hakan a Legas a ranar Laraba. Ya ce za a yi zaben 2023 lafiya kalau kuma Kwankwaso ne da jam'iyyar za su yi nasara.

Kara karanta wannan

Magudi akayi min a 2019, ni na lashe zabe: Atiku Abubakar

Allah ne ya aiko Kwankwaso ya fatattaki yunwa, ya hada kan 'yan Najeriya, NNPP
Allah ne ya aiko Kwankwaso ya fatattaki yunwa, ya hada kan 'yan Najeriya, NNPP. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC
"Ya kasance a rubuce, ba Kwankwaso bane kadai batun. Gaskiyar lamarin, taimakon Ubangiji ya zo Najeriya a lokacin da zaben 2023 ke gabatowa.
"A don haka ne muke sanar da cewa, Sanata Kwankwaso ne Ubangiji ya aiko domin ya hada kan 'yan Najeriya kuma ya fara tun daga tushe.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Muna gayyatar jama'ar Najeriya da su garzayo jam'iyyar mu domin gina Najeriyar da muke mafarki," Agubanze yace.

The Nation ta ruwaito cewa, ya jinjinawa Sanata Orji Kalu, tsohon gwamnan jihar Abia kuma jigon APC da yace bayyanar Kwankwaso ya sauya tsarin siyasar Najeriya kafin zuwan zaben 2023.

Kamar yadda yace, Kalu ya jaddada cewa za a yi zabe lafiya kalau kuma Sanata Kwankwaso zai yi nasara da jam'iyyar.

"A yayin da muka saurari kalamansa na shawarwari ga jam'iyyarmu, mun gano cewa 'yan Najeriya suna bukatar bayyanar sabon al-fijir.

Kara karanta wannan

APC da PDP sun fi karfin talaka da matasa: Adamu Garba ya sayi fom din takara a YPP

"Sanannen abu ne ga duk wani mai kishin kasa kuma dan Najeriya mai hankali da ya gane cewa sunan jam'iyyar NNPP da logon kayan marmari daga Ubangiji ne.
"Abinda za mu iya cewa ga 'yan Najeriya kai tsaye shi ne, babu mai ba ka mulki, don haka mu tabbatar mun yi rijista da INEC tare da bai wa kuri'unmu kariya.
"Mu yi hakan saboda buge gwarzo a kowanne gasa akwai wahala amma ana iyawa," ya kara da cewa.

Hotuna: Shekarau ya dawo jam'iyyar mu, kwankwaso ya taya shi murna, NNPP

A wani labari na daban, jam'iyyar NNPP ta ce Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan jihar Kano sannan sanata mai ci, ya dawo jam'iyyar.

Cigaban yazo ne bayan wasu kwanaki da Abdulmumin Jibrin, tsohon 'dan majalisar dattawa kuma babban daraktan kungiyar kamfen din Bola Tinubu ya shiga jam'iyyar, The Cable ta ruwaito.

Canza shekar da Jibrin ya yi ta tabbata duk da kokarin da Abdullahi Ganduje, gwamnan jihar Kano, yayi don kangeshi daga barin jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Daga Karshe, Shekarau Ya Fita Daga APC, Ya Koma NNPP Ya Haɗe Da Kwankwaso

Asali: Legit.ng

Online view pixel