Ba zan yi amai na lashe ba: Martanin gwamna Wike da ya sha kaye bayan ganawa da Atiku

Ba zan yi amai na lashe ba: Martanin gwamna Wike da ya sha kaye bayan ganawa da Atiku

  • Gwamna Wike na jihar Ribas ya bayyana goyon bayansa ga Atiku bayan da ya sha kaye a zaben fidda gwnain PDP
  • Wike ya bayyana cewa, PDP dai tasu ce, kuma ba zai bari ko ya yi watsi da muradin jam'iyyar ta adawa ba
  • Ya bayyana haka ne jim kadan bayan da Atiku ya kai masa ziyarar neman goyon bayan lashe zaben fidda gwani

Abuja - Gwamnan jihar Ribas kuma tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Nyesom Wike, ya jaddada cewa zai cika alkawarinsa ta hanyar marawa dan takarar shugaban kasa a PDP Alhaji Atiku Abubakar baya.

Wike a ranar Asabar jim kadan kafin a fara kada kuri’a a zaben fidda gwanin PDP ya yi alkawarin tallafa wa duk wanda ya samu nasara daga cikin masu neman tsayawa takara a jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Atiku ya sa labule da Gwamna Wike bayan lallasa shi a zaɓen fid da gwanin PDP

Martanin Wike bayan ganawa da Atiku
2023: Martanin wanda ya sha kaye a zaben fidda gwanin PDP bayan ganawa da Atiku | Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Jaridar Leadership ta rahoto cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku ya lashe zaben fidda gwanin takarar shugaban kasa da kuri’u 371 inda ya doke abokin takararsa mai bi masa, Gwamna Wike wanda ya samu kuri’u 237.

Bayan haka, a ranar Litinin ne Atiku ya bi har gida, ya ziyarci Wike a Abuja domin neman goyon bayan gwamnan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sa’o’i kadan bayan haka, Gwamna Wike, a shafinsa na Twitter ya yi martani game ziyarar Atiku, ya ce PDP jininsu ne, kuma ba zai yi watsi da muradinta ba, don haka zai marawa tsohon mataimakin shugaban kasar baya kamar yadda ya yi alkawari.

Gwamna Wike ya rubuta cewa:

“Na yi alkawari ga Jam’iyyar PDP ta Najeriya cewa zan mara wa duk wanda ya fito daga takarar zaben fidda gwani na #PDP, kuma ba zan yi amai na lashe ba.

Kara karanta wannan

Ayu ga Tambuwal: Kai ne gwarzon babban taron jam'iyyar PDP

"Ba za mu iya watsi da turbar PDP ba, za mu ci gaba da marawa Atiku Abubakar baya."

Tsohon dan takara a PDP ya lashe tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour

A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, ya karbi tikitin takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour, rahoton jaridar Punch.

Hakan na zuwa ne bayan da wani dan takarar shugaban kasa a dandalin jam’iyyar, Farfesa Pat Utomi, ya amince da marawa Obi baya, wanda ya koma jam’iyyar a makon jiya.

Utomi, wanda fitaccen farfesa ne a fannin tattalin arziki, ya yanke amincewa janyewa Obi a ranar Litinin a wurin da aka gudanar da zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar a Delta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel