Atiku, Obi, NNPP da wasu abubuwa 5 da Kwankwaso ya yi magana a hirar da aka yi da shi

Atiku, Obi, NNPP da wasu abubuwa 5 da Kwankwaso ya yi magana a hirar da aka yi da shi

  • A ranar Litinin ne aka yi wata hira ta musamman da Rabiu Musa Kwankwaso a gidan Channels TV
  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi bayanin inda ya sa gaba a siyasa da kuma irin manufofinsa
  • Babban ‘dan siyasar ya samu damar yin karin haske a kan wasu zargi da ake yi masa a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bibiyi wannan hira, ta kuma tsakuro muhimman batutuwan da aka yi magana a kai:

1. NNPP

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi bayani kan kafuwar NNPP tun a 2001 da zaburowarta a yanzu, ya kuma tabbatar da shi kadai ne wanda ya saye fam.

2. Haduwa da Peter Obi

Rabiu Musa Kwankwaso ya tabbatar da cewa sun zauna da Peter Obi sun tattauna bayan barinsa PDP, amma ba su gama magana a kan takara ba, sai ya shiga LP.

Kara karanta wannan

Ban matsu dole sai na zama shugaban ƙasa a 2023 ba, Kwankwaso ya magantu

An ji labari ba don Obi ya samu takarar shugaban kasa a jam’iyyar LP ba, watakila da zai zama abokin takarar Rabiu Kwankwaso a karkashin jam’iyyarsu ta NNPP.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

3. Zargin bangaranci da murkushe Kudu

Tsohon Gwamnan na Kano ya musanya zargin cewa yana da bangaranci da kokarin neman mulki duk da ya fito daga Arewa maso yamma da ke kan mulki.

Kwankwaso ya ce abin da ake bukata shi ne kwarewar mutum, ya ce ‘yan siyasa na yaudarar jama’a domin daga 1960, babu yankin da bai mulki kasar nan ba.

4. Ra’ayin zafin kishin addini

A Najeriya babu wanda ya sha wahala a kan lamarin addini irin Rabiu Musa Kwankwaso a cewarsa, ya ce zargin bai yarda da shari’a ba ta sa ya sha kashi a 2003.

A hirar, Kwankwaso ya ce idan mutum yana siyasa, babu irin zargin da mutane ba za su yi masa ba. A cewarsa, yanzu siyasarsa ta shiga ko ina, har a kasashen ketare.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi magana a kan zargin yi wa Wike ko wani ‘dan takara aikin boye a PDP

Rabiu Musa Kwankwaso
Jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: @mohd.saifullahi.9
Asali: Facebook

5. Ruguza kasuwar Legas

Ba a kare zantawa da Kwankwaso ba sai da aka yi maganar ruguza kasuwar Alaba rago a Legas, ya bayyana kokarin da yake yi na ganin ba a rusa wannan kasuwa ba.

Sanata Kwankwaso zai nemi ya gana da Gwamnan jihar Legas a kan batun bayan an kawo masa kuka, ya ce raba mutane da hanyar cin abicinsu yana da matukar hadari.

6. Akidar Kwankwasiyya

Babban abin da ke gaban Kwankwaso a tsarinsu shi ne talakawa, ‘dan siyasar ya ce abin da suka koya wajen Malam Aminu Kano shi ne gwamnati ta taimaki mara karfi.

7. Yi wa Buhari da Atiku aiki

Rabiu Kwankwaso ya ce ya yi wa Muhammadu Buhari aiki a zaben 2015 duk da sun nemi takara tare a APC, haka zalika Atiku Abubakar a PDP a zaben da ya wuce na 2019.

Za a ji Kwankwaso yana cewa bai dauki mulki dole ba, don haka ne ya je har gida ya taya Ibrahim Shekarau murna a 2003, ya kuma ki zuwa kotu domin ya yi karar zaben.

Kara karanta wannan

Halin da Atiku, Saraki, Tambuwal, da Wike suke ciki a wajen zaben zama ‘dan takaran PDP

8. Zaben fitar da gwani da 2023

A karshen wannan tattaunawa, tsohon Ministan tsaron ya yarda zai yi masa wahala ya lashe zaben fitar da gwani a irin siyasarsa, amma ya ce zai iya doke kowa a 2023.

Matasan Daura sun yi na'am

Labari ya zo mana a ranar Litinin cewa wasu matasan da ke yankin Daura a Arewacin Katsina sun yi zama da jagororin Jam’iyyar NNPP yayin da ake shirye-shiryen zabe.

A wajen wannan taro, an yi kira na musamman ga matasa su zabi Rabiu Kwankwaso a 2023. Muttaqa Darma ya ce Kwankwaso zai taimaki matasa idan ya karbi mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel