Ban matsu dole sai na zama shugaban kasa a 2023 ba, Sanata Kwankwaso

Ban matsu dole sai na zama shugaban kasa a 2023 ba, Sanata Kwankwaso

  • Sanata Rabiu Kwankwaso ya ce shi ba wai ya matsa ta dole sai ya zama shugaban ƙasa a zaɓen 2023 da ke tafe
  • Jagoran NNPP na ƙasa ya ce shi da makamantansa da suka shiga jam'iyyar, sun yi haka ne domin ceto yan Najeriya
  • Ya ce kowane cikakken mai kishin ƙasa ya damu da yanayin tsaro, tattalin arziki kuma yana bukatar samun shugaba nagari

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce shi bai da matsanancin burin dole sai ya zama shugaban kasa a zaɓen 2023.

Jagoran jam'iyyar NNPP na ƙasa ya yi wannan furucin ne yayin zantawa da kafar watsa labarai Channels tv ranar Litinin 30 ga watan Mayu, 2022.

Ya ce shi da kuma masu kyakkyawar zuciya sun shiga New Nigeria Peoples Party wato (NNPP) ne domin canza halin da ake ciki da kuma ceto Najeriya daga rushewa.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Yan bindiga sun kashe tsohon kwamishinan NPC ta ƙasa, sun sace 'ya'yansa mata

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Ban matsu dole sai na zama shugaban kasa a 2023 ba, Sanata Kwankwaso Hoto: Dailytrust.com
Asali: UGC

Daily Trust ta rahoto Kwankwaso na cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Abin da yan Najeriya ke cewa shi ne suna bukatar nagari a kowane lokaci, ni zan iya baku tabbacin cewa Ni ba mutum bane da ya matsu dole sai ya zama shugaban ƙasa."

Mutane sun haji ya kamata a canza - Kwankwaso

Kwankwaso, wanda ke neman ɗare wa kujerar shugaban ƙasa karƙashin NNPP ya kara da cewa mutane sun gaji da tsohon tsari kuma suna bukatar canji.

"Mun gaji da tsohon tsarin da ake amfani da shi yau, shiyasa muka rungumi NNPP domin kawo canji, yadda abubuwa ke wakana a kasar nan yanzu ya yi muni."
"Kowane mutum ya damu da halin tsaro, tattalin arziki ya raunata, dukan sassan ilimi da al'adu, komai dai ya lalace. Haka ne maƙasudin da ni da makamanta na muka shiga NNPP, muna bukatar haɗuwa wurin ɗaga kudu da arewa"

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi magana a kan zargin yi wa Wike ko wani ‘dan takara aikin boye a PDP

"Abin da yan Najeriya ke cewa shi ne a 2023, suna son shugaban ƙasa da ya cancanta, mutum mai gaskiya da rikon Amana, wanda zai iya aikin da ake bukata."

A wani labarin na daban kuma Gwamna Wike ya faɗi yanda ya so yamutsa zaben fidda gwanin PDP bayan sake ba Tambuwal dama

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya nuna rashin jin daɗinsa da matakin barin Tambuwal ya sake jawabi har ya janye wa Atiku.

A cewar Wike, bayan ya gama jawabinsa duk bai san da janyewa ba, sai dai kaunarsa ga PDP ta sa ya zuba wa zuciyarsa ruwan sanyi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel