Matasan Daura su na goyon bayan Kwankwaso ya karbi mulkin Najeriya bayan Buhari

Matasan Daura su na goyon bayan Kwankwaso ya karbi mulkin Najeriya bayan Buhari

  • Wasu matasan da ke yankin Daura a Arewacin Katsina sun yi zama da jagororin Jam’iyyar NNPP
  • A wajen wannan taro, an yi kira na musamman ga matasa su zabi Rabiu Musa Kwankwaso a 2023
  • Haka zalika an tallata takarar gwamnan Nura Khalil a jihar Katsina a wannan taro da aka yi a Daura

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Katsina - Gangamin kungiyoyin matasa da ke shiyyar Daura da ke jihar Katsina, sun nuna su na goyon-bayan Rabiu Musa Kwankwaso ya karbi mulki.

Rahoton da ya fito daga Daily Nigerian ya bayyana cewa wadannan matasa sun yi kira ga mutanen yankin Daura da su zabi Dr. Rabiu Kwankwaso.

Matasan sun yi wannan kira a wajen wani taro da aka yi a ranar Lahadi, 29 ga watan Mayu 2022 domin marawa Injiniya Nura Khalil baya a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Gwamnan Borno a 2023: Dan takarar PDP ya zargi Zulum da son kai, ya sha alwashin tsige sa daga mulki

Injiniya Nura Khalil yana cikin masu neman takarar gwamna a jihar Katsina a karkashin NNPP.

Daya daga cikin jagororin APC, Muttaqa Rabe Darma ya ce makasudin taron shi ne yi wa matasan yankin na Daura bayanin manufofin masu takarar gwamna.

Kwankwaso zai yi da matasa

A cewar Injiniya Muttaqa Rabe Darma, idan aka zabi Sanata Kwankwaso a matsayin shugaban Najeriya a 2023, za a maida hankali wajen cigaban matasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwankwaso a Legas
Lokacin da Kwankwaso ya ziyarci Legas Hoto: @mohd.saifullahi.9
Asali: Facebook

“Idan za ku iya tunawa, a lokacin da yake Gwamnan jihar Kano, ya taimakawa matasa da dama sun yi karatu a Najeriya da kasashen waje.”
“Bayan haka, a lokacin da yake gwamna bayan ya kammala wa’adinsa, ya dauki nauyin karatun mutanen jihar Kano domin su karo karatu.”
“Wasu daga cikinsu su na aiki, wasu su na amfani da abin da suka koya a sanadiyyarsa.”

Kara karanta wannan

2023: Dattijo ya lashe tikitin APC na sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya

“Ya kafa cibiyoyin koyon sana’a a kananan hukumomi 44 da ke Kano, ga masu bukatar iya sana’a, idan ya samu mulki, zai cigaba da wannan.”

PM News ta ce jagoran matasan da suka halarci taron, Bashir Bala ya yi irin wannan kira, ya yabi irin rawan da Darma ya taka sa'ilin yana rike da hukumar PTF.

NNPP ta shiga Katsina

Kwanaki kun samu labari daga bakin tsohon Sanatan Katsina, Abdu Umar ‘Yandoma cewa an nada Alhaji Gambo Salisu a matsayin sabon shugaban NNPP.

Abdu Umar ‘Yandoma wanda ya taba wakiltar yankin Daura a majalisar dattawa, yana cikin jagororin jam'iyyar APC da ke burin karbe mulki a hannun APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel