Tsohon dan takara a PDP ya lashe tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour

Tsohon dan takara a PDP ya lashe tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour

  • Bayan ficewa daga jam'iyyar PDP gabanin zaben fidda gwani, Peter Obi ya koma jam'iyyar Labour, ya samu tikitin takara
  • Ya samu tikitin gwabzawa da 'yan takara a sauran jam'iyyu a 2023 ne bayan da Pat Utomi ya janye daga takara
  • Jam'iyyun siyasa na ci gaba da gudanar da zabukan fidda gwani a kasar nan yayin da ake shirye-shiryen zaben 2023

Delta - Tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, ya karbi tikitin takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour, rahoton jaridar Punch.

Hakan na zuwa ne bayan da wani dan takarar shugaban kasa a dandalin jam’iyyar, Farfesa Pat Utomi, ya amince da marawa Obi baya, wanda ya koma jam’iyyar a makon jiya.

Peter Obi ya lashe takarar shugaban kasa
Yanzu-Yanzu: Peter Obi ya lashe tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a Labour | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Utomi, wanda fitaccen farfesa ne a fannin tattalin arziki, ya yanke amincewa janyewa Obi a ranar Litinin a wurin da aka gudanar da zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar a Delta.

Kara karanta wannan

An hana yan jarida shiga: APC na cigaba da tantance yan takararta na shugaban ƙasa a Abuja

Sai dai SaharaReporters ta samu labarin cewa Utomi ne ya taka rawar gani wajen ganin Obi ya koma jam’iyyar Labour daga PDP.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Utomi ya sanar da cewa Obi matashi ne mai fafutuka tare da ikon aiwatar da canjin da ake bukata a tsarin Najeriya.

Har ila yau, wani dan takarar mai shekaru 45, Joseph Faduri ya janyewa tsohon gwamnan duk dai a wurin zaben fidda gwanin.

Obi wanda ya kasance dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, ya fice daga jam’iyyar sannan kuma ya fice daga takarar shugaban kasa a dandalin jam’iyyar a ranar 25 ga watan Mayu.

APC: Dan majalisan Arewa da ake zargi da badakalar kudin Korona ya rasa tikitin tazarce

A wani labarin na daban, Godday Odagboyi, dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Apa/Agatu, ya sha kaye a yunkurinsa na sake tsayawa takara a zaben 2023 mai zuwa, TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da duminsa: EFCC ta gurfanar da Rochas Okorocha kan zargin damfarar N2.9bn

Odagboyi wanda ya tsaya takarar neman tikitin takarar Sanata na jam’iyyar APC ya sha kaye a hannun Adama Adama, hamshakin dan kasuwa wanda aka fi sani da Otalaka.

Da yake sanar da sakamakon a ranar Asabar, shugaban kwamitin zabe Franklin Shagbaor, ya ce Adama ya samu kuri’u 21,747 inda ya doke Odagboyi wanda ya samu kuri’u 3,151.

Asali: Legit.ng

Online view pixel