Da Dumi-Dumi: Jam'iyyar APC ta tantance yan takarar shugaban ƙasa da ke son gaje Buhari

Da Dumi-Dumi: Jam'iyyar APC ta tantance yan takarar shugaban ƙasa da ke son gaje Buhari

  • Jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar nan ta fara aikin tantance yan takararta na shugaban ƙasa
  • Bayanai sun nuna cewa an hana yan jarida shiga wurin tantancewa, kuma kwamitin ya fara da tsohon karamin ministan ilimi
  • Kwamitin tantancewa karkashin jagorancin tsohon shugaban APC na kasa, John Oyegun

Abuja - Jam'iyyar All Progressive Congress wato APC ta fara aikin tantance yan takarar shugaban ƙasa waɗan da ke yunkurin gaje shugaba Buhari a zaɓen 2023.

Tantancewar ta fara gudana ne a sirrance a wani shahararren Hotel 'Transcorps Hilton Hotel' da ke babban birnin tarayya Abuja.

Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, da sauran jagororin jam'iyya mai mulki tuni suka mamaye wurin, kamar yadda Channels tv ta tabbatar.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta tantance gwamnan Jigawa, Tinubu da Amaechi sun dira wurin a Abuja

Tantance yan takarar shugaban ƙasa.
Da Dumi-Dumi: Jam'iyyar APC ta tantance yan takarar shugaban ƙasa da ke son gaje Buhari Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Tsohon gwamnan Ogun kuma sanata mai wakiltar mazaɓar Ogun ta tsakiya, Sanata Ibikunle Amosun, wanda na ɗaya daga cikin yan takara, yana cikin mutanen da suka isa wurin don tantancewa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wata majiya ta shaida wa jaridar cewa Kwamitin da zai tantance yan takarar shugaban ƙasan na APC yana ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan Ogun kuma tsohon shugaban APC na ƙasa, Mista John Oyegun.

An hana yan jarida shiga

Daily Trust ra rahoto cewa an hana manema labarai shiga wurin, amma wasu bayanai sun nuna cewa tsohon ministan ƙaramin ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, shi ne mutum na farko da aka tantance.

Kuma bayan kammala tantance shi, bai yarda ya zanta da manema labarai ba, a halin yanzun ana cigaba da tantance yan takara.

Ragowar yan takarar da za'a tantance

Yan takarar da ake tsammanin tantancewa sun haɗa da, Bola Tinubu, Farfesa Yemi Osinbajo, Godswill Akpabio, gwamna Yahaya Bello, Ibikunle Amosun, Gwamna Kayode Fayemi, Rochas Okorocha.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Cikin 'yan tawagar Tinubu ya duri ruwa, yayin da ake ci gaba da tantance 'yan takara

Sauran sune; Sanata Ahmad Lawan, Gwamna Dave Umahi, gwamna Abubakar Badaru, Gwamna Ben Ayade, Fasto Tunde Bakare, Ken Nnamani, Rotimi Amaechi, Ogbonnaya Onu, Sani Yeriman Bakura, da Ikeobasi Mokelu.

Sai kuma yar takara ɗaya kuma mace ɗaya tilo, Uju Ohanenye, Nicholas Felix, Dimeji Bankole, Tein Jack da sauran su.

A wani labarin kuma Bayan shan kaye hannun Atiku, Gwamnan arewa ya fara shirin kwace tikitin takarar gwamna a jiharsa

Bayan rashin nasara a zaɓen fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa, Gwamna Bala Muhammed na Bauchi ya fara shirin tazarce a kujerarsa

Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa dama can akwai 'Plan B' idan har gwamnan bai samu nasara ba a zaɓen fidda gwani ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel