Karin bayani: EFCC ta gurfanar da Rochas Okorocha kan zargin damfarar N2.9bn

Karin bayani: EFCC ta gurfanar da Rochas Okorocha kan zargin damfarar N2.9bn

  • Hukumar yaki da rashawa da hana yi wa kasa ta'annati, ta gurfanar da Sanata Rochas Okorocha a gaban kotu
  • Hukumar ta gurfanar da shi ne a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja kan zargin laifuka 17 da suka hada da almundahanar N2.9b
  • An damke dan takarar shugabancin kasan a makon da ya gabata bayan jami'an EFCC sun zagaye gidansa na sa'o'i shida

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi watattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta gurfanar da dan takarar shugabancin kasa na APC daga jihar Imo, Rochas Okorocha, a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Okorocha, wanda a halin yanzu ya ke wakiltar mazabar Imo ta yamma a majalisar dattawa, an gurfanar da shi gaban mai shari'a Inyang Ekwo a ranar Litinin, Channels Tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Kotu ta ba EFCC umarnin ci gaba da garkame sanata bisa zargin rashawa

Da duminsa: EFCC ta gurfanar da Rochas Okorocha kan zargin damfarar N2.9bn
Da duminsa: EFCC ta gurfanar da Rochas Okorocha kan zargin damfarar N2.9bn. Hoto daga channelstv.com
Asali: UGC

Ana tuhumarsa da laifuka 17 da suka hada da damfara kudi da ta kai N2.9 biliyan wanda hukumar EFCC ta shigar a kansa.

Hukumar EFF cat gufanar da Okorocha tare da Chinenye da wasu kamfanoni biyar - Naphtali International Limited, Perfect Finish Multi Projects Limited, Consolid Projects Consulting Limited, Pramif International Limited, and Legend World Concepts Limited - kan wasu zarge-zarge da suka hada da kwashe kudin jihar Imo yayin da ya ke gwamnan jihar kudancin kasar nan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Okorocha da Chinenye sun musanta aikata laifukan da ake zarginsu kuma kotun ta rubuta hakan bisa bukatar lauyanzu, Darlington Ozurumba.

Sanye dashudiyar malum-malum da hula ruwan kasa, an shigo da Okorocha dakin kotun kafin karfe 9 na safe tare da jami'an EFCC.

Jami'an tsaro sun budewa magoya bayan Okorocha wuta a farfajiyar gidansa

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: EFCC ta sake bankado wata badakalar biliyan N90 kan Akanta-Janar, ya zama biliyan N170

A wani labari na daban, jami'an tsaro da ke zagaye da gidan tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, a Abuja sun bude wa magoya bayan dan majalisar wuta domin tarwatsa su.

Masu zanga-zangar wadanda da yawansu mata ne da manema labarai da ke kula da cigaban, a halin yanzu suna gudun ceton rayukansu.

Jami'an tsaron suna jaddada cewa ba za su bar farfajiyar gidan ba har sai an damke dan siyasar, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel