Jonathan ba ‘Dan Jam’iyyarmu ba ne, ba za mu ba shi takara ba inji Mataimakin Shugaban APC

Jonathan ba ‘Dan Jam’iyyarmu ba ne, ba za mu ba shi takara ba inji Mataimakin Shugaban APC

  • Salihu Lukman ya yi watsi da rade-radin cewa Goodluck Jonathan zai yi takara a jam’iyyar APC
  • Mataimakin shugaban jam’iyyar ta APC na Arewa ya tabbatar da Dr. Goodluck Jonathan bai da rajista
  • Lukman ya yarda komai zai iya faruwa, ya sha alwashi idan yana nan, ba za a ba Jonathan tikiti ba

Abuja - Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na shiyyar Arewa maso yamma, Salihu Lukman ya ce sam Dr. Goodluck Jonathan bai cikin ‘ya ‘yan jam’iyyarsu.

Salihu Lukman ya bayyana wannan ne a lokacin da Punch ta yi hira da shi ta wayar salula a jiya.

Mataimakin shugaban jam’iyyar mai mulki ya tabbatar da cewa Goodluck Jonathan bai cikin ‘ya ‘yansu, kuma su na mamaki da rade-radin takararsa a 2023.

Kara karanta wannan

2023: Babu ruwan Buhari da shirin ba Jonathan takara a APC inji Fadar Shugaban kasa

A cewar Salihu Lukman, ba su da labarin cewa akwai wani wanda ya saye fam din neman zama shugaban kasar Najeriya a zaben 2023 da sunan Dr. Jonathan.

Jonathan bai cikin 'Yan APC

“Zan iya fada maka wannan kai-tsaye. Jonathan bai cikin ‘ya ‘yan APC, a iyakacin abin da jam’iyyar ta sani.”

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Abin da ake tattaunawa a kai (neman takarar shugaban kasa) a gidajen yada labarai, abin mamaki ne a wurinmu.”
“Ba mu da labarin wani ya saye fam din shiga takara da sunan Jonathan, kuma mun rufe kofar saida fam."

- Salihu Lukman

Jonathan bai cikin APC
Dr. Goodluck Ebele Jonathan Hoto: jonathangoodluck
Asali: Facebook

Lukman ya ce duk jita-jita ce kurum ke yawo, ko da cewa ya san komai zai iya faruwa a Najeriya.

Sai dai a halin da jam’iyyar APC mai mulki ta samu kanta a ciki, Lukman ya ce ba zai yiwu ta ba Jonathan takarar shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa ba.

Kara karanta wannan

Jerin abubuwa 10 da suka jawo Atiku Abubakar ya dankara Wike da kasa a zaben PDP

Idan har ina ofis ... - Lukman

“Za ku iya cewa ni na fadi wannan a ko ina, ba zai taba yiwuwa ba. Duk mai wannan maganar, shirme kurum yake fada.”
“Rade-radi ne, ko da komai zai iya faruwa a kasar nan, amma idan irinmu na rike da mukamai a jam’iyya, ba za ta yiwu ba."

- Salihu Lukman

Rahoton ya ce Lukman ya nuna za a fito da ‘dan takara ne ta hanyar zaben gwani, ba maslaha ba.

APC na kwadayin Jonathan?

A baya kun samu rahoto cewa gabannin zaben fidda dan takarar shugaban kasa na APC, jam’iyyar mai mulki ta na ci gaba da zawarcin Goodluck Jonathan.

Wata majiya ta nuna cewa APC na kokarin ganin tsohon shugaban kasa Jonathan ya zama wanda zai daga tutarta a babban zabe na 2023 mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel