Jerin abubuwa 10 da suka jawo Atiku Abubakar ya dankara Wike da kasa a zaben PDP

Jerin abubuwa 10 da suka jawo Atiku Abubakar ya dankara Wike da kasa a zaben PDP

  • Alhaji Atiku Abubakar ya sake zama ‘dan takarar shugaban Najeriya a karkashin jam’iyyar PDP
  • Da kuri’u 371, tsohon mataimakin shugaban Najeriyan ya doke Nyesom Wike da ya samu kuri’a 237
  • Ratar kuri’a 134 aka samu tsakanin Wazirin Adamawa da Gwamnan jihar Ribas wanda ya zo na biyu

A wannan rahoto, mun tattaro abubuwan da suka taimaka wajen ba Wazirin Adamawa nasara:

1. Aminu Tambuwal

The Cable ta ce Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya taka rawar gani wajen nasarar Atiku Abubakar duk da cewa da farko ya tsaya a kan bakarsa.

Tambuwal ya umarci mutanensa su zabi Atiku, wannan ta sa ya ba gwamnan Ribas tazara da kyau.

2. Boye ‘yan jam’iyya

Da yake tsohon ‘dan siyasa ne, Atiku Abubakar ya tara mutanensa 275, ya boye su a otel dinnan na the Sheraton Abuja domin gudun a canza masu ra’ayi.

Kara karanta wannan

Zaben fidda dan takarar shugaban kasa na PDP: Jerin yan takarar da basu samu kuri’a ko daya ba

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Dan takarar ya hana kowa haduwa da ‘ya ‘yan jam’iyyar da ya tabbata za su kada masa kuri’a. Wannan dabara ta yi aiki bana, akasin yadda aka yi a 2014.

3. Ortom – Ayu - Mark

Jaridar ta ce da farko, an yi tunani Gwamnan Benuwai, Samuel Ortom na tare da Nyesom Wike, bayan Iyorchia Ayu ya karbi PDP, sai abubuwa suka bayyana.

Da Gwamnan na Benuwai da Iyorchia Ayu da kuma David Mark duk mutanen Benuwai ba su nunawa takarar Atiku adawar da Nyesom Wike yake sa rai ba.

4. Hana daukar hoto

Jam’iyyar PDP ta haramtawa masu kada kuri’a daukar hoto bayan sun zabi ‘dan takara. Hana zuwa da wayar salula da kwamiti ya yi, ta taimaki Atiku Abubakar.

Wannan ya sa wasu ‘yan jam’iyya musamman daga Arewa suka karbi kudin wasu ‘yan takaran, amma ba su zabe su ba, kuma ba za a iya gane wannan yaudarar ba.

Kara karanta wannan

Halin da Atiku, Saraki, Tambuwal, da Wike suke ciki a wajen zaben zama ‘dan takaran PDP

Atiku Abubakar ya ci zaben PDP
Atiku Abubakar ya yi nasara a PDP Hoto: Atiku.org/Abban Hajia
Asali: Facebook

5. Tsohon hannu

Tun 1992 dai Atiku Abubakar ya fara neman takarar shugaban kasa, har yau kuma da shi ake damawa a siyasa, sannan ya rike mataimakin shugaban Najeriya.

Legit.ng Hausa ta fahimci ya fi sauki sauran ‘yan takara su goyi bayan Atiku Abubakar, a kan ya zama shi ne zai sallama ganin girma da darajarsa a siyasar yau.

6. Atiku ya kafu

Premium Times ta ce Atiku Abubakar ya kafu a siyasar kasar nan don haka babu wanda zai iya ja da shi tsakaninsu Nyesom Wike, Bukola Saraki ko kuma Pius Anyim.

7. Barin kofa a bude

Legit.ng Hausa ta fahimci rashin ware takara zuwa yankin kudancin Najeriya shi ne babban abin da ya yi sanadiyyar da mutumin kudu bai samu tikitin takara ba.

Kwamitin Samuel Ortom ya bada shawarar a bar kowane yanki ya nemi kujerar shugaban kasa a zaben 2023 ba, wannan ya karya ‘yan siyasar kudancin Najeriya.

Kara karanta wannan

Tsohon Hadiman Buhari da ke takara a Kano ya fice, ‘yan daba sun cika wajen zaben APC

8. Arewa

Daily Trust ta ce jihohin Arewa sun zarce na yankin kudu a yawa, hakan ta sa zai yi wa mutum irin Atiku Abubakar samun kuri’u daga wajen mutanen yankinsa.

Akwai masu zaben ‘dan takarar shugaban kasa fiye da 400 daga shiyyar Arewa, yayin da kudu ke da 300. Nyesom Wike bai samu kuri’u masu tsoka daga Arewa ba.

9. Sa bakin manya

An ji Janar Aliyu Gusau da Attahiru Bafarawa sun yi kokarin shawo kan Tambuwal wanda yake da kuri’u sosai daga Arewa maso yamma da yankin jihar Imo.

Sa bakin da manyan Arewa suka yi, ya yi amfani wajen ganin an hana ‘yan kudu samun tikitin 2023.

10. Kudi

Atiku Abubakar kasurgumin attajiri ne wanda ya gawurta a kasuwanci. Zaben tsaida gwani musamman a irin PDP sai da kudi, Wazirin Adamawa ya na da su.

Legit.ng Hausa ta fahimci ana zargin tsohon mataimakin shugaban kasar da sauran ‘yan takara sun yi rabon Dalolin kudi, wannan ya taimaka wajen nasarar Atiku.

Kara karanta wannan

Zaben fidda gwani: An sanar da wanda ya lashe tikitin takarar gwamnan APC a Sokoto

Kwankwaso na tare da Wike?

Ana da labari Rabiu Musa Kwankwaso ya nesanta kansa da zargin hada-kai da Nyesom Wike wajen samun takarar Najeriya a karkashin jam'iyyar adawa ta PDP.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce babu abin da ya hada shi da PDP tun da ya bar jam’iyyar. Ana zargin ya karbi kudi ne daga hannun Gwamnan na jihar Ribas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel