2023: Babu ruwan Buhari da shirin ba Jonathan takara a APC inji Fadar Shugaban kasa

2023: Babu ruwan Buhari da shirin ba Jonathan takara a APC inji Fadar Shugaban kasa

  • Wata majiya daga Fadar shugaban kasa ta nuna babu maganar ba Goodluck Jonathan takaran 2023
  • Ana ta rade-radin Dr. Goodluck Jonathan ne ake so a tsaida takarar shugaban kasan 2023 a APC
  • Wasu na kusa da Aso Rock Villa sun tabbatar da cewa Muhammadu Buhari bai goyon bayan hakan

Abuja - Fadar shugaban kasar Najeriya ta nesanta Mai girma Muhammadu Buhari da zargin ba Goodluck Jonathan takara a jam’iyyar APC a zaben 2023.

Wata majiya ta shaidawa The Nation cewa babu yadda za ayi shugaba Muhammadu Buhari ya goyi bayan Goodluck Jonathan ya zama ‘dan takaran APC.

Buhari wanda ya saba caccakar gwamnatin jam’iyyar PDP ba zai marawa jam’iyyarsa baya ta tsaida wanda shi da kan sa ya tika shi da kasa a 2015 ba.

Majiyar ta shaidawa jaridar cewa hadiman tsohon shugaban kasar ne suke yada jita-jitar, su na nuna hotunan mai gidan na su tare da Muhammadu Buhari.

Wani lokaci mutanen Jonathan su ka yi ta yama-didi da hotunan Goodluck Jonathan a duk lokacin da ya ziyarci shugaban Najeriyan ko na kusa da shi.

Duk da Buhari bai fadawa Duniya matsayarsa a kan wanda ya kamata ya gaji mulki a hannunsa ba, wani da ke Aso Villa ya ce babu Jonathan a lissafinsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Fadar Shugaban kasa
Shugaba Buhari da Jonathan Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC
“Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan bai cikin lissafin ko kadan.”
“Ambatan sunansa da ake yi ya jawowa Aso Villa abin kunya da jin wani bambarakwai.”

- Majiyar Aso Rock

Wannan rahoto ya zo a jaridar Sun na ranar Litinin, majiyar labarin bai bari an kama sunan shi ba.

Jaridar ta fahimci har ta kai an bada umarni a fadar shugaban kasa ka da a sake fito da hoton haduwar Goodluck Jonathan da magajinsa, Muhammadu Buhari.

A matsayinsa na wanda ya taba rike mulki, duk lokacin da ya ga dama, Jonathan zai iya neman ganawa da shugaban Najeriya a fadar Aso Rock Villa da ke Abuja.

Ana sa ran cewa da zarar jam’iyyar APC ta gudanar da zaben ‘dan takarar shugaban kasa a mako mai zuwa, kowa zai fahimci gaskiyar rade-radin da yake ta yawo.

Jonathan ba 'Dan APC ba ne

Labari ya zo mana cewa mataimakin shugaban APC na bangaren Arewa maso yamma, Salihu Lukman ya yi watsi da rade-radin Goodluck Jonathan zai yi takara.

Mataimakin shugaban jam’iyyar mai mulki ya tabbatar da cewa Goodluck Jonathan bai cikin ‘ya ‘yansu, kuma su na mamaki da jin rade-radin neman takararsa a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel